An Rasa Rai, Yan Sanda Sun Jikkata da Aka Farmaki Ofishin Jakadancin Isra’ila
- Rahotanni da dama sun bayyana an kashe mutum daya yayin harin bindiga kusa da ofishin jakadancin kasar Isra’ila
- ‘Yan sanda biyu sun jikkata yayin da jami’an tsaro suka shiga yankin bayan harbin bindiga yayin da ake yaki a Gabas ta Tsakiya
- Isra’ila ta yi gargadin karuwar barazanar hare-hare kan ‘yan kasarta a kasashen waje inda ta bayyana shirin daukar matakai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Istanbul, Turkey - Majiyoyi sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun kai wani hari a ofishin jakadancin Isra'ila da ke birnin Istanbul a kasar Turkiyya.
An ce mutum daya ya mutu yayin da wasu biyu suka jikkata a wani harin bindiga da aka kai kusa da ofishin jakadancin Isra’ila da ke Istanbul a kasar Turkiyya.

Source: Facebook
An kai hari a ofishin jakadancin Isra'ila

Kara karanta wannan
Babu sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a garuruwa 12 na kasar Musulunci
Gwamnan Istanbul, Davut Gul, ya ce harin ya kuma jikkata ‘yan sanda biyu, duk da cewa raunukan ba su da tsanani, cewar rahoton CNN.
An ga jami’an rundunar musamman ta Turkiyya sun mamaye yankin bayan an ji karar harbin bindiga na wani lokaci.
Wani jami’in Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ya bayyana cewa ofishin jakadancin ba ya dauke da ma’aikata a lokacin da lamarin ya faru.
Abin da Turkiyya ta ce kan harin Istanbul
Ministan shari’a na Turkiyya, Akin Gurlek, ya tabbatar da cewa an fara bincike kan harbin da ya faru a kusa da ofishin da ke yankin Beşiktaş na Istanbul.
An ce ofishin jakadancin yana hawa na bakwai ne a wani gini da ke wannan yanki wanda lamarin ya tayar da hankulan mutane da ke kusa da wurin.
Rahotanni sun ce an ji karar harbin bindiga a kusa da ginin da ke dauke da ofishin jakadancin Isra’ila.

Source: Getty Images
Korafin da Isra'ila ke yi kan farmakin Yahudawa
A gefe guda, hukumomin Isra’ila sun bayyana cewa an samu karuwar yunkurin kai hare-hare kan ‘yan kasarta da Yahudawa a kasashen waje tun bayan fara rikicin Iran.
Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta yi kakkausar suka kan abin da ta kira “harin ta’addanci da aka kai kan ofishin jakadancin Isra’ila a Istanbul, cewar rahoton BBC.
Sanarwar ta ce:
“Muna godiya ga jami’an tsaron Turkiyya bisa saurin daukar mataki wajen dakile wannan hari.
“Ofisoshin jakadancin Isra’ila a fadin duniya suna fuskantar barazana da hare-haren ta’addanci masu yawa. Ta’addanci ba zai hana mu ci gaba da ayyukanmu ba.”
Yemen ta shiga yakin Iran gadan-gadan
A wani labarin, mun ba ku labarin cewa rundunar sojojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ta kakkabo wani makami mai linzami da aka harbo daga ƙasar Yemen a ranar Alhamis 2 ga watan Afrilun 2026.
Sautin ƙararrawar gargadi ya cika biranen Isra'ila yayin da take ke fuskantar ruwan makamai masu linzami daga Iran, Yemen da Lebanon a yakin da ake yi.
A gefe guda, sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa sun kashe Jamshid Eshaqim, babban kwamandan hedikwatar man fetur na Iran yayin da yaki ke kara kamari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
