Matakin da Gwamnati Ta Ɗauka kan Ɗan Amurka da Ke 'Tunzura Kiristoci' a Jos
- Gwamnatin Tarayya ta kori wani ɗan ƙasar Amurka, Alex Barbir, saboda zargin yin kalaman rarraba kawuna da tunzura jama'a a jihar Filato
- Wata jami'ar fadar shugaban ƙasa ta alaƙanta Barbir da kisan wasu Musulmai mutum biyu da aka yi a birnin Jos jim kaɗan bayan wani jawabi da ya yi
- Gwamnati ta kwatanta ayyukan Barbir da abubuwan da suka janyo kisan kiyashin Rwanda, inda ta jaddada cewa ba za ta bar hakan ta faru ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da korar wani mai ɗan Amurka, Alex Barbir, daga Najeriya bisa zargin yin kalaman tunzura jama’a da za su iya haddasa mummunan tashin hankali a kasar.
Babbar Mataimakiya Ta Musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan harkokin hulɗa da al’umma, Abiodun Essiet, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin.

Source: Twitter
Gwamnati ta kori d'an Amurka, Alex Barbir
A wata hira da gidan talabijin na TVC News, Abiodun Essiet ta jaddada cewa ayyukan Barbir sun zama babbar barazana ga haɗin kan Najeriya, musamman a yankin Arewa ta Tsakiya dake fama da rikice-rikice.
Misis Essiet ta bayyana cewa tuni aka fitar da Ba'amurken daga ƙasar domin dakatar da abubuwan da yake ƙullawa, musamman na tunzura Kiristoci su dauki doka a hannu.
Ta bayyana cewa:
“Haka ne, mun fahimci abubuwan da Alex Barbir yake ƙullawa, don haka ya kamata in sanar da ku cewa Alex Barbir ba ya Najeriya a halin yanzu.”
Ta ƙara da cewa an fitar da shi ne saboda ayyukan rarraba kawuna da yake yi waɗanda suka fara haifar da zubar da jini.
A cewarta, jim kadan bayan Barbir ya yi wani jawabi a birnin Jos, aka kashe Musulmai biyu, wanda hakan ke nuna irin haɗarin da kalaman nasa ke da shi.
Darasi daga kisan kiyashin Rwanda
Gwamnatin tarayya ta bayyana fargabar cewa kalaman Barbir na iya jefa Najeriya cikin irin halin da ƙasar Rwanda ta tsinci kanta a 1994.
Essiet ta ce abin da Alex Daniel Barbir yake faɗa kusan iri ɗaya ne da dabarun da aka yi amfani da su wajen raba kan ƙabilun Hutu da Tutsi har ta kai ga an yi yakin kisan kiyashi.
Ta gargaɗi ƴan Najeriya da kada su bar mutanen da ba su san tarihin ƙasar ba su shigo suna raba kansu, tana mai kira da a zauna lafiya.

Source: Twitter
Alex Barbir ya yi martani ga Essiet
Sai dai, Alex Barbir, a shafinsa na X, ya karyata dukkan abubuwan da Abiodun Essiet ta fada a kansa, inda ya ce:
"Ba gaskiya ba ne: Idan har Abiodun Essiet, babbar mai tallafa wa Shugaban kasa Bola Tinubu ta yi wannan maganar, to lallai tana shirga karya ne ga 'yan Najeriya da kasashen waje.

Kara karanta wannan
Yaki ya rincabe: Iran ta harba makamai 300 lokaci 1 kan sojojin Amurka da Isra'ila
"Ni ban ma taba sanin wannan baiwar Allah ba, kuma ban taba yin magana da su ba. Ofishin jakadancin Amurka ya riga ya karyata wannan ikirari."
Dan Amurka na yawo a kauyukan Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, masana da masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun fara magana kan wani dan kasar Amurka, Alex Birbir da ke yawo a kauyukan Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa Alex Birbir na shiga kauyuka ne a jihohin Arewa ta Tsakiyan Najeriya da sunan wa'azi da wayar kan Kiristoci.
Yawon da Alex Birbir ke yi ya fara daukar hankali ne bayan ganin shi a wajen da aka kai hari aka kashe mutane da dama a cikin dare a Filato.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

