Abba Ya Zabi Wanda zai Zama Kwamishinan Rikon Kwarya bayan Tafiyar Hon. Umar Doguwa
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Dr. Dahir Hashim a matsayin mukaddashin ma'aikatar da Umar Haruna Doguwa ya bari
- Umar Haruna Doguwa, shi ne kwamishinan ma'aikatar ruwa ta jihar Kano kafin ya yi murabus domin zama shugaban jam'iyyar APC na Kano
- Sabon kwamishinan rikon wanda matashi ne ya yi alƙawarin inganta samar da ruwa mai tsafta ga al’ummar Kano da suka a dade suna cikin kunci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dr Dahiru Muhammad Hashim, a matsayin mukaddashin kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa ta jihar.
An bayyana wannan mataki ne a ranar Litinin 7 ga watan Afrilu, 2027, inda Dr. Hashim ya tabbatar da nadin tare da bayyana godiya ga gwamnan Kano.

Source: Facebook
A cikin sakon, da ya wallafa a shafin Facebook, ya ce wannan ƙarin nauyi da aka ɗora masa alama ce ta amincewar da gwamnatin jihar ke da ita a kansa.
Gwamnan jihar Kano ya yi nadi
Dr. Dahiru Hashim ya ce gwamnan ya ba shi wannan dama ne domin ya jagoranci harkokin ma’aikatar albarkatun ruwa tare da aikinsa na kwamishinan muhalli da sauyin yanayi.
A cewarsa:
“Mai girma gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙara ɗora min alhakin zama mukaddashin kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa ta jihar.”
Rahotanni sun nuna cewa Dr. Dahiru Hashim ya amince da cewa aikin da ke gabansa ba ƙarami ba ne, musamman wajen magance ƙalubalen samar da ruwa a faɗin jihar Kano.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa zai yi aiki da ƙwazo da jajircewa domin ganin an samu sauƙi a harkar samar da ruwa mai tsafta da aminci ga mazauna jihar.
A cewarsa, za a riƙa samun ci gaba ne a hankali, amma da tabbacin cewa ana ɗaukar matakai masu ɗorewa domin warware matsalolin da ke akwai.
Mukaddashin Kwamishinan Kano ya yi addu'a
Mukaddashin kwamishinan ya kuma yi addu’ar neman taimakon Allah domin samun jagora da ƙarfi wajen sauke nauyin da aka ɗora masa.
Wannan naɗi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan more rayuwa a jihar Kano, musamman a ɓangaren samar da ruwa, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga lafiyar al’umma da ci gaban tattalin arziki.
Tsohon kwamishinan ya bar kujerarsa ne domin ya zama shugaban jam'iyyar APC na reshen Kano.
Gwamnatin jihar na sa ran wannan sabon tsarin jagoranci zai taimaka wajen kawo sauyi mai ma’ana a ma’aikatar albarkatun ruwa tare da inganta ayyukan da suka shafi samar da ruwa ga jama’a.
Gwamna Abba Kabir ya gana da Shekarau
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf na ƙara zama domin jawo Sanata Ibrahim Shekarau zuwa jam'iyyar APC mai ci.
Sauye-sauyen siyasa da aka fara gani a jihar sun rikita tafiyar jam’iyyu a Kano gabanin babban zaben 2027 musamman bayan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya koma ADC.
Tattaunawa ta gudana a ɓoye kan yiwuwar sauya sheƙar Shekarau, yayin da jam'iyyu ke rububin ya dawo cikinsu saboda tasirinsa a siyasar Kano da Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


