Matasa Sun Dauki Mataki Mai Muni da Aka Kashe Wani Bawan Allah kan 'Pure Water' a Katsina

Matasa Sun Dauki Mataki Mai Muni da Aka Kashe Wani Bawan Allah kan 'Pure Water' a Katsina

  • Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon cacar bakin da ta auku a shagon wani Inyamuri a garin Kokami da ke karamar hukumar Danja a Katsina
  • Rahoto ya nuna cewa mai shagon ya caka wa wani Ibrahim Auwal almakashi har lahira, hakan ya fusata matasa suka dauki mataki a fusace
  • Gwamnatin Danja karkashin Hon. Rabo Tambaya ta yi Allah wadai da lamarin, kuma ta dauki matakan dawo da doka da oda a garin Kokami

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Wani rikici da ya auku kan cinikin garri da ruwan leda (pure water) ya yi sanadin mutuwar mutane biyu a ƙauyen Kokami da ke Karamar Hukumar Danja a Jihar Katsina.

Lamarin wanda ya afku a ranar Asabar, 4 ga watan Afrilu, 2026, ya raba Ibrahim Auwal da wani mai shago, Joe (wanda aka fi sani da K.C. Jones) da rayukansu.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe budurwa da harbin bindiga tana shirin tafiya aure a Borno

Danja.
Takardar sanya dokar hana fita a Kokami, da Ahugaban karamar hukumar Danja, Rabo Tambaya Hoto: Usman Bandiro
Source: Facebook

Yadda lamarin ya faru a kauyen Katsina

Rahoton Premium Times ya nuna cewa rashin jituwa ta barke ne tsakanin mutanen biyu a shagon Mista Jones, inda ake zargin ɗan kasuwar ya soki Ibrahim Auwal da almakashi yayin da suke cacar baki.

An garzaya da Ibrahim zuwa Asibitin Abdullahi Makama da ke garin Dabai, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

Bayan samun labarin rasuwar Ibrahim, wasu mutanen garin sun harzuƙa inda suka dauki doka da hannunsu kan Mista Jones, suka kashe shi, sannan suka ƙona gawarsa a gefen titi.

Matakin da gwamnatin Danja ta dauka

Tuni dai gwamnatin karamar hukumar Danja karkashin jagorancin Hon. Rabo Tambaya ta sanya dokar hana fita daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safiya a Kokami.

Hadimin shugaban karamar hukumar Danja, Hon. Usman Badiro ya tabbatar da hakan, tare da turo wa wakilin Legit Hausa kwafin takardar sanya dokar ta manhajar Whatsapp.

Kara karanta wannan

Rikicin Jos ya rutsa da Ibrahim, an kashe matashi ɗan NYSC daga yin aurensa

Ya ce Mai Girma Rabo Tambayo ya yi Allah wadai da lamarin kuma gwamnatinsa ta dauki duk matakan da suka dace domin kwantar da hankula da kuma dawo da doka da oda.

Ya ce:

"Mun samu labarin wani ne ya je sayayya shagon Jones, wani inyamuri da ke kasuwancin a garin, sai rigima ta hada su, ya dauki makami ya caka masa, hakan ya yi sanadin mutuwarsa.
"Su kuma matasa ransu ya baci, suka je suka fasa shagon suka kamo Jones, suka kashe shi.
"Yanzu dai gwamnati ta sa dokar hana fita don shawo kan lamarin. Daukar doka a hannu ba abu ne mai kyau ba, gwamnatin Danja ta yi Allah wadai da lamarin."

Yan sandan Katsina sun cafke mutum 4

Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina ta sanar da cewa ta yi nasarar kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa ɗan kasuwar, kamar yadda Channels tv ta kawo.

Dakarun yan sanda.
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, kakakin rundunar, Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa jami'ansu sun isa wurin cikin gaggawa kuma sun dawo da doka da oda.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban Amurka, Trump ya 'kori' Antoni Janar ana tsaka da yakin Iran

Ya ƙara da cewa: "Wadanda ake zargin suna tsare, kuma ana ci gaba da bincike."

Kwamishinan Yan Sanda, Ali Fage, ya yi Allah wadai da wannan danyen aiki, inda ya yi kira ga mazauna yankin da su riƙa kai koke-kokensu ga hukumomin tsaro maimakon ɗaukar doka a hannunsu.

Mutane sun mutu a wurin rabon zakkah

A wani rahoton, kun ji cewa an rasa rayuka yayin rabon Zakkar Ramadan a gidan wani attajiri da ke Kofar Guga a jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa akalla mutum hudu ne suka mutu yayin da wasu 18 suka samu raunuka a turmutsitsin da aka yi wajen rabon Zakkah.

Jami’an ‘yan sanda na Katsina sun gaggauta isa wurin, inda suka samu nasarar shawo kan lamarin tare da dawo da soka ta oda.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262