Hatsabibin Ɗan Bindiga, Ado Allero Ya Tafka Rashi, Sojoji Sun Kashe Ɗan Cikinsa

Hatsabibin Ɗan Bindiga, Ado Allero Ya Tafka Rashi, Sojoji Sun Kashe Ɗan Cikinsa

  • Sojojin Operation FANSAN YANMA sun hallaka fitattun shugabannin 'yan bindiga da dama ciki har da ɗan babban jagoran 'yan ta'adda Ado Aliero
  • An yi amfani da jiragen yaƙi da dakarun ƙasa wajen murƙushe ƴan fashin dajin kusan 300 da suka yi ƙoƙarin tunkarar sojojin a cikin daji
  • Masana tsaro sun yi gargaɗin cewa Ado Aliero na iya ƙoƙarin ɗaukar fansar mutuwar ɗan nasa, wanda hakan ya sa aka ƙarfafa tsaro a Zamfara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Zamfara – Sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da ƴan fashin daji, inda ta kashe aƙalla ƴan ta’adda 65 a wani gagarumin samame da aka kai a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara .

Dakarun rundunar Operation FANSAN YANMA ne suka ƙaddamar da wannan hari na haɗin gwiwa tsakanin dakarun ƙasa da na sama a ƙauyen Munhaye dake bayan Kunchin Kalgo.

Kara karanta wannan

Abba Kabir ya magantu kan tasirin APC a Kano, ya yi wa Tinubu babban alƙawari

Sojoji sun kashe d'an hatsabibin jagoran 'yan bindiga, Ado Aliero
Jagoran 'yan bindiga, Ado Aliero yana jawabi a wani taron sulhu. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Facebook

An kashe ɗan babban ɗan ta'adda Ado Aliero

Wannan samame ya yi sanadiyyar mutuwar fitaccen jagoran 'yan fashin daji, Kachalla Iliya Sarki, wanda ɗa ne ga babban ɗan ta'adda Ado Aliero dake addabar Arewa maso Yamma, in ji rahoton Zagazola Makama.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar wa Zagazola Makama cewa artabun ya fara ne da misalin ƙarfe 6:00 na daren ranar Asabar kuma aka kwashe sa'o'i bakwai ana fafatawa.

Ado Aliero ya tattaro 'yan ta'adda kusan 300 a kan babura daga yankin Yan Wari, sannan ya samu ƙarin mayaka daga sansanin Dankarami Gwaska domin tunkarar sojoji.

Duk da yawan ƴan ta’addan, dakarun soji sun nuna musu fifikon makamai da dabarun yaƙi, kamar yadda wata majiyar tsaro ta tabbatar.

Baya ga ɗan Ado Aliero, majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an kashe wasu kwamandojin kamar Dogo Sule da Iliya Mai Rasha.

Fargabar daukar fansa daga Ado Aliero

Kara karanta wannan

"Allah na fushi da Kwankwaso," NNPP ta fadi dalilin rikicin da ya taso a ADC

Abin takaici shi ne, dakarun sa-kai guda bakwai da suka yi yaƙi kafa-da-kafa tare da sojoji sun riga mu gidan gaskiya a yayin wannan fafatawa.

Rahotanni sun nuna cewa Ado Aliero ya tsere ya buya a garin Yankuzu, yayin da sojoji ke ci gaba da bin sahu domin ruguza ragowar ƙungiyarsa baki ɗaya yau.

Wani manazarcin tsaro ya bayyana cewa:

"Wannan babbar nasara ce ga aikin soja. Mutuwar Iliya Sarki za ta gurgunta tsarin bayar da umarni a cikin ƙungiyar ɓarayin."

Sai dai jami'an tsaro sun yi gargaɗin cewa Aliero na iya ƙoƙarin ɗaukar fansa, inda aka nemi karin sa ido sosai a ƙauyukan da basu da kariya domin kare su daga hare-harensa.

Sojoji na ci gaba da gudanar da ayyukan kakkabe 'yan ta'adda a Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara, inda sojoji suka kashe dan hatsabibin jagoran 'yan ta'adda, Ado Aliero. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wanene Kachalla Iliya Sarki?

Iliya Sarki ya kasance ɗaya daga cikin kwamandojin ɓarayi mafi muni dake gudanar da garkuwa da mutane da satar shanu a jihohin Katsina, Zamfara, har ma da sassan jihar Kano.

Kwanaki huɗu kacal kafin mutuwarsa, an ce ya tafi har jihar Kano domin yin satar shanu, wanda hakan ke nuna girman tasirin ɓarnarsa, in ji rahoton The Whistler.

Kara karanta wannan

Wuya ta yi wuya: Isra'ila ta dakatar da kai hare hare kan kasar Iran, an ji dalili

Kashe shi babban koma-baya ne ga ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso Yamma. Rundunar soji ta tabbatar da cewa tana nan tana ci gaba da bincike da kakkabe daji domin tabbatar da cewa ba a bar wani ɗan ta'adda a yankin ba.

Kanin Ado Aliero ya kai hari Katsina

A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya daga Birged ta 17 da ke Jihar Katsina ta samu nasarar kwato dabbobi 529 da ‘yan ta’adda suka sace.

An kaddamar da wannan aiki ne ta hannun dakarun Forward Operating Base (FOB) Malumfashi, bayan samun sahihan bayanan sirri kan wasu ‘yan bindiga a yankin Kasuwan Sabo da ke Kafur.

'Yan ta’addan sun shigo yankin ne daga Jihar Zamfara, kuma ana zargin wani mai suna Idi Abasu Aiki, kanin shahararren jagoran ‘yan bindiga Ado Aliero, ne ya jagorance su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com