An Kashe fiye da Mutane 10, An Kone Gidaje 50: Halin da Ake ciki a Nasarawa
- Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai mummunan hari kauyukan jihar Nasarawa, inda suka kashe fiye da mutane 10 tare da kona fiye da gidaje 50
- Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da cewa harin na ramuwar gayya ne bayan zargin kisan wasu mutane biyu daga bangaren maharan
- 'Dan majalisar yankin ya bayyana cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 15, yayin da wasu mutane da dama har yanzu ba a san inda suke ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Nasarawa – Jihar Nasarawa ta sake fuskantar wani mummunan tashin hankali bayan da wasu 'yan bindiga suka kaddamar da hari kan garuruwan Akyawa da Udege Kasa dake karamar hukumar Nasarawa.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya tabbatar da harin a ranar Asabar, inda ya ce harin ya faru ne a ranar Juma'a.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun kashe mutane a Nasarawa
A cewarsa, wannan danyen aiki ya faru ne a matsayin ramuwar gayya sakamakon zargin kisan wasu mutane biyu daga kabilar maharan da aka yi a baya, in ji rahoton The Cable.
Harin ya bar baya da kura, inda maharan suka kona gidaje fiye da 50, motoci, babura, da kuma rumbunan abinci na mazauna yankin.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Shetima Mohammed, ya ziyarci wurin inda ya nuna juyayi tare da yin alkawarin kamo dukkan wadanda ke da hannu a wannan kisan kiyashi.
Da yake jawabi ga iyalan wadanda abin ya shafa, Kwamishinan ya ce:
"Ina mika ta'aziyyata ga iyalan mamata da daukacin al'ummar wannan yankin, sannan ina tabbatar muku da kudurin rundunarmu na tabbatar da cewa adalci ya yi aiki."
Sabani kan adadin wadanda suka mutu
Duk da cewa 'yan sanda sun ce mutum 11 ne suka mutu, dan majalisa mai wakiltar mazabar Udege/Loko, Onarigu Onah, ya bayyana cewa adadin ya haura hakan.
Bayan ziyarar gani da ido da ya kai kauyukan Udege Kasa da Odeni Gida, ya tabbatar da cewa mutane kusan 15 ne aka kashe, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Onah ya bayyana harin a matsayin abin takaici, inda ya ce:
"Wannan hari na baya-bayan nan ya kai ga mutuwar mutane kusan 15, yayin da wasu har yanzu ba a san inda suke ba."

Source: Original
Matakan maido da zaman lafiya
Dan majalisar ya jajantawa wadanda abin ya shafa, inda ya tabbatar musu da cewa zai hada hannu da hukumomi domin tabbatar da tsaron rayuka yau.
"Zan hada hannu da shugaban karamar hukumar da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi," in ji Onarigu Onah.
A halin yanzu, rundunar 'yan sandan ta ce an riga an maido da doka da oda a kauyukan da abin ya shafa. Jami'an tsaro na ci gaba da sintiri a dazuzzukan kewayen kauyukan domin tabbatar da cewa maharan ba su sake dawowa ba.
An rasa rayuka a Nasarawa
A wani labari, mun ruwaito cewa, ’yan bindiga sun kai harin ta'addanci a kauyen Kunza, cikin gundumar Ashigye da ke karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan
2027: Jerin ministoci da manyan jami’an gwamnatin Tinubu 7 da suka yi murabus don takara
'Yan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Talata, 30 ga watan Disamban 2025 inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama.
Majiyoyin sun yi zargin wasu sun yi wa Fulani Makiyaya biyu kwanton bauna a kusa da wata gada da ke yankin Akunza–Ashigye, inda aka ce daya daga cikinsu ya rasu.
Asali: Legit.ng

