Rikici tsakanin Tubabben Ɗan Boko Haram da Jam'in Tsaro Ya Jawo Asarar Rai
- Wani tsohon ɗan Boko Haram da ya tuba ya samu mummunan sabani da jami'in tsaron sa kai na CJTF a jihar Borno
- Rikici yayi tsanani a lokacin da tubabben dan Boko Haram din ne rike da bindiga kirar AK-47 a hannunsa
- Mutum guda ya rasa ransa, kuma jami’an tsaro sun kama wanda ake zargi tare da mika shi ga hukuma yayin da ake bincike a Maiduguri
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Wani mummunan lamari ya auku a ƙaramar hukumar Mafa da ke jihar Borno, inda wani tsohon ɗan ƙungiyar Boko Haram da ya tuba samu hatsaniya da jami'in CJTF.
Ana tsaka da wannan hatsaniya sai tsohon ɗan Boko Haram din ya fusata, ya saita kirjin jami'in tsaron na sa kai, ya sakar masa kumar bindiga.

Source: Original
Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa majiyoyin tsaro sun tabbatar masa lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Afrilu, 2026 da 10.16 na safe a garin Mafa.
Tsohon ɗan Boko Haram ya kashe jami'i a Borno
Daily Post ta wallafa cewa sabani ya ɓarke tsakanin mutanen biyu, wanda daga bisani ya rikide zuwa rikici mai muni da ya yi asarar ran jami'in tsaron CTJF a Borno.
Bayanan da aka tattara sun nuna cewa wanda ake zargi, mai suna Abba Gana mai shekaru 20, tsohon ɗan Boko Haram ne da ya tuba kuma yake aiki ƙarƙashin tsarin CJTF.

Source: Twitter
Ana zarginsa da harbe Adamu Ali, mai shekaru 25, a ƙirji da bindigar AK-47 yayin da suke cacar baki kan batun da ba a bayyana ko menene ba.
Nan take aka garzaya da Adamu Ali zuwa Babban Asibitin Mafa domin ceto rayuwarsa, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa bayan isarsa asibitin.
Hankalin mutanen Borno ya tashi
Lamarin ya tayar da hankali a yankin, musamman ganin cewa duka biyun suna cikin tsarin haɗin gwiwar tsaro da aka kafa domin taimaka wa jami’an gwamnati wajen yaƙar ta’addanci a arewa maso gabas.
Bayan aukuwar lamarin, kwamandan CJTF a ƙaramar hukumar Mafa, Abba Sadu, ya tabbatar da kama wanda ake zargi, inda aka mika shi ga rundunar ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.
Majiyoyin tsaro sun kuma bayyana cewa an kai ziyara wurin da lamarin ya faru domin duba yanayi da tattara hujjojin da za a yi amfani da su.
Haka kuma, an ɗauki hotunan wurin tare da kwato bindigar da aka yi amfani da ita a matsayin shaida.
Sashen binciken manyan laifuffuka (CID) da ke Maiduguri ya fara zurfafa bincike domin gano cikakken dalilin da ya haddasa rikicin da ya kai ga wannan kisa.
Hukumar tsaro na ci gaba da ƙoƙarin fahimtar ko akwai wasu dalilai na ɓoye da suka haddasa wannan rikici, musamman dangane da yadda tsofaffin ‘yan Boko Haram da suka tuba ke mu’amala da sauran jami’an tsaro da fararen hula.
An kama John, ɗan Boko Haram a Adamawa
A baya, kun ji cewa dakarun Najeriya sun kama wasu mutane da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne da ke kai hare-hare a Arewa maso Gabashin Najeriya.
Daga cikin wadanda aka kama akwai mai suna John Ado da ya amsa cewa yana tallafawa kungiyar, inda ya fadi wuraren da suka kai hari da kashe mutane.
John Ado ya bukaci jami'an tsaro su sake shi domin a cewar shi ya tuba, kuma zai ba gwamnati hadin kai wajen tona asirin 'yan ta'addan da ya riƙa aiki da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


