An Kama Mai Suna 'John' cikin Masu kai Hari a Kungiyar Boko Haram
- Dakarun Najeriya sun kama wasu mutane da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne da ke kai hare-hare a Arewa maso Gabashin Najeriya
- Cikin wadanda aka kama akwai mai suna John Ado da ya amsa cewa yana tallafawa kungiyar, inda ya fadi wuraren da suka kai hari
- John Ado ya bukaci jami'an tsaro su sake shi domin a cewar shi ya tuba, kuma zai ba gwamnati hadin kai wajen tona asirin 'yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa - Dakarun sojin Najeriya sun kama John Ado da wasu mutum biyu da ake zargi ‘yan Boko Haram ne a ƙauyen Balda da ke Ƙaramar Hukumar Gombi a Jihar Adamawa.
Hakan na zuwa ne yayin da jami'an tsaro suke cigaba da bibiyar 'yan ta'addan domin kakkabe su da kawo karshen su a fadin Najeriya.

Source: Facebook
Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa an cafke waɗanda ake zargin ne a ranar 29 ga Maris, 2026 yayin wani samame da ake ci gaba da yi na yaƙi da ta’addanci, kamar yadda ya wallafa a X.
An kama John cikin 'yan Boko Haram
Majiyoyi tsaro sun ce mutane biyun da aka kama tare da John Audu na daga cikin mayaƙan ƙungiyar ta’addanci da ake zargin suna da hannu a hare-hare a wasu sassan Kudancin jihar Borno.
A yayin binciken farko, waɗanda ake zargin sun amsa cewa aikinsu shi ne tattara kayan da aka wawashe yayin hare-hare, ba wai suna shiga fagen daga kai tsaye ba.
Rahotanni sun nuna cewa sun amince cewa suna kula da kayayyakin da aka kwaso daga hare-haren da aka kai a Ngoshe, maimakon su shiga gaba wajen faɗa.

Source: Original
An shirya kai hari Mubi a Adamawa
Majiyoyin sun ƙara da cewa bayanan sirri da aka samu daga gare su sun nuna shugabanninsu sun shirya kai hari wani barikin sojoji a Mubi domin satar abubuwan fashewa.
Sun ce shirin ya kuma haɗa da amfani da waɗannan abubuwan fashewa wajen lalata wata gada da ke kan Kogin Benue a Yola, domin hana zirga-zirga da kuma gurgunta harkokin tattalin arziki.
Boko Haram: Bayanin John Audu
A bayanin da ya yi, John Audu ya sanar da cewa ba su san adadin mutanen da aka kashe a Ngoshe ba amma ya san an kashe mutane da dama.
Ya ce yana cikin 'yan sa-kai amma yana ba 'yan Boko Haram bayanai, sai dai ya ce wuka ya rike ba bindiga ba a harin da aka kai Ngoshe.
Ga bidiyon bayanin da suka yi a kasa:
An kama sojin bogi a Filato
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama wani sojan bogi bayan kai mummunan hari a Filato.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun sun kuma kama wani matashi dauke da bindigogin gida da ake zargin za a yi aiki da su wajen kai hari.
Hakan na zuwa ne bayan wani hari kan mai uwa da wabi da wasu 'yan bindiga da ba a gano su waye ba suka kai unguwar Rukuba a Jos.
Asali: Legit.ng

