Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane har da Sace Jami'an Tsaro a Sokoto
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani kauye da ke karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto
- Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba yayin harin wanda suka kai a cikin tsakar dare
- Hakazalika, 'yan bindigan sun yi awon gaba da jami'an tsaro na 'yan sa-kai tare da wasu mutane ciki har da mata da yara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari garin Achida da ke Ƙaramar Hukumar Wurno a Jihar Sokoto.
'Yan bindigan sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da aƙalla mutane 25 a yayin harin.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis, 2 ga watan Afirilun 2026 a cikin garin wanda ke da tazarar kusan kilomita 20 daga birnin Sokoto.
'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare, inda suka kwashe kusan sa'a guda suna cin karensu baka ba tare da wani ƙalubale ba.
Yayin harin, an bayar da rahoton cewa 'yan bindigan sun kashe mazauna garin guda biyu tare da kwashe wasu da dama, ciki har da mata, yaro ɗan shekara 10, da kuma mambobin ƙungiyar sa-kai.
Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun fara farmakar wurin jami'an sa-kai ne da ke wajen garin.
“Sun kewaye jami'an sa-kanmu da ke kan aikinsu, suka yi garkuwa da su kafin su shiga cikin gari don kwashe mata da ƙananan yara daga gidajensu."
- Wata majiya
'Yan bindiga sun kashe mutane
A cewar mazaunin garin, maharan sun gudanar da aikin ne cikin tsanaki, sai bayan sun kammala kwashe mutanen ne suka fara harbi, wanda hakan ya jefa jama'a cikin firgici.
“Ba mu san da zamansu ba sai kusan tsakar dare lokacin da aka fara jin ƙarar harbe-harbe. A lokacin ne aka kashe mutanenmu guda biyu."
- Wani mazaunin garin
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa 'yan bindigan sun rarrabu ne, wasu sun tsaya a wajen gari don lura da yiwuwar shigowar sojoji, yayin da sauran suka kwashe mutanen.

Source: Original
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Legit Hausa ta yi kokarin tuntuɓar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, domin samun karin bayani kan lamarin.
Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa bai samu rahoton ba amma zai bincika ya gani.
"Ban samu wannan rahoton ba amma zan bincika na gani."
- DSP Ahmad Rufai
'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma.
'Yan bindigan sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane waɗanda ba a tantance adadinsu ba a harin da suka kai a kauyen Dangoro da ke karamar hukumar Bungudu.
Maharan sun cinna wa gidaje da dama da rumbunan hatsi wuta, lamarin da ya tilasta wa mazauna Dangoro da dama tserewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


