Rikicin Jos Ya Rutsa da Ibrahim, an Kashe Matashi Ɗan NYSC bayan Aurensa

Rikicin Jos Ya Rutsa da Ibrahim, an Kashe Matashi Ɗan NYSC bayan Aurensa

  • Wani mummunan al’amari ya faru a Jos inda aka kashe wani dan bautar ƙasa mai shekaru 31 a duniya bayan aurensa
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa matashin ya rasa ransa ne kwanaki biyu kacal kafin kammala hidimarsa bayan aure da ya yi
  • An ce Ibrahim Haruna Abdulkareem ya mutu ne bayan harin ramuwar gayya a Anguwan Rukuba inda ‘yan bindiga suka kai farmaki tare da kashe mutane

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Wani mummunan lamari ya girgiza Jos inda aka kashe wani matashin dan bautar ƙasa a birnin da ke jihar Plateau.

Marigayin mai suna Ibrahim Haruna Abdulkareem ya rasa ransa kwanaki biyu kafin ya kammala hidimarsa ta kasa.

Matashi ya rasa ransa a harin ramuwar gayya a Jos kwana 2 kafin kammala NYSC
Matashi Ibrahim Haruna da rikicin Jos ya rutsa da shi a Plateau. Hoto: @___Bils.
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa matashin yana da shekaru 31 kuma ya yi aure wata takwas da suka wuce yayin da yake shirin kammala bautar ƙasa ta NYSC.

Kara karanta wannan

Rasuwar jigon APC na Kano ta tada hankali, an ji yadda ya rasu a otal a Abuja

Yadda yan bindiga suka yi ta'asa a Jos

Rahotanni sun nuna cewa an kashe shi ne a lokacin wani hari na ramuwar gayya a Anguwan Rukuba da ke Jos ta Arewa, inda ‘yan bindiga suka afkawa mazauna yankin,wanda aka tabbatar da mutuwar mutane akalla 28 a harin.

Marigayin, wanda ke zaune a unguwar Yantifa, yana aiki a makarantar Almustafa a matsayin wurin aikinsa na NYSC.

Haka kuma yana yin aikin achaba domin kara samun kudin tallafawa iyalinsa da sauran yan uwansa daidai gwargwado.

Kanin marigayin, Mustafa Haruna Abdulkareem, ya bayyana cewa dan uwan nasa ya fita aiki da misalin karfe 7:00 na yamma, amma daga baya suka ji labarin harin, sun yi ta kokarin kiransa amma wayarsa ba ta shiga.

Ya ce daga baya ne tare da taimakon kungiyoyi kamar JNI da Red Cross da jami’an tsaro aka tabbatar musu cewa an kashe shi, lamarin da ya jefa iyalin cikin matsanancin bakin ciki da jimami.

Kara karanta wannan

Trump ya gindaya sharudan tsagaita wuta, ya fadi rokon da Iran ta yi masa

Yadda harin ramuwar gayya ya yi ajalin matashi
Taswirar jihar Plateau da aka samu rikicin addini a Jos. Hoto: Legit.
Source: Original

Martanin mahaifiyar marigayin da aka kashe

An kuma bayyana cewa gawarsa ta lalace matuka, wanda ya sa aka takaita halartar jana’izarsa ga mutum daya daga cikin iyali domin kaucewa tashin hankali a al’umma.

Mahaifiyarsa, Zainab Hassan, ta ce mutuwarsa babban rashi ne gare su domin shi ne dan ta na fari kuma kadai mai digiri a cikin iyali.

Ta kara da cewa kudin alawus din NYSC ba su wadatar, shi ya sa ya shiga aikin achaba domin taimaka wa matarsa mai ciki da sauran ‘yan uwa, cewar Sahara Reporters.

Iyalan sun kuma bayyana cewa marigayin ya bar mata mai ciki wata bakwai, wacce yanzu za ta fuskanci rayuwa ba tare da mijinta ba yayin da suke neman gwamnati ta tabbatar da adalci.

JNI ta magantutu kan Musulmi da aka kashe

Kun ji cewa rahotannin da suka fito daga kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) sun bayyana adadin Musulman da aka kashe a wani hari da aka kai a Plateau.

Kara karanta wannan

Matakai 2 da Tinubu ya dauka da aka kashe Musulmai da Kiristoci a Jos

Hakan na zuwa ne bayan wasu 'yan ta'dda sun kai harin mai uwa da wabi kan jama'a da dare a jihar Plateau, sama da mutum 20 suka mutu.

A yanzu haka dai kungiyar JNI ta sanar da cewa akalla Musulmai 10 ne ba a san a ina suke ba tun bayan harin da aka kai kuma ana neman su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.