Rasuwar Jigon APC na Kano Ta Tada Hankali, An Ji Yadda Ya Rasu a Otal a Abuja

Rasuwar Jigon APC na Kano Ta Tada Hankali, An Ji Yadda Ya Rasu a Otal a Abuja

  • Mataimakin sakataren tsare-tsaren APC na Kano, Abdulsalami Ginsau ya rasa ransa a lokacin babban taron jam'iyya da aka gudanar a Abuja
  • Bayanai sun nuna cewa jigon na APC ya rasu ne a cikin wata matattakalar lantarki da ta lalace a otal din da aka sauke wakilan jihar Kano
  • Iyalan marigayin sun nemi a gudanar da bincike domin tabbatar da abin da ya yi ajalin Ginsau, wanda suka ce ya bar gida cikin koshin lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Bayanai na kara fitowa game da rasuwar mataimakin sakataren tsare-tsare na APC ta Kano, Abdulsalami Ginsau, wanda ya riga mu gidan gaskiya a otal din Chida da ke Utako a Abuja.

Ginsau, wanda lauya ne, shi ne ya jagoranci kwamitin da aka dorawa alhakin shirya masauki ga wakilan APC daga Jihar Kano da suka halarci babban taron jam'iyya na kasa.

Kara karanta wannan

Matakai 2 da Tinubu ya dauka da aka kashe Musulmai da Kiristoci a Jos

Abdulsalami Ginsau
Marigayi mataimakin sakataren tsare-tsaren APC na Kano, Abdulsalami Ginsau Hoto: Zainabu Abu
Source: Facebook

Yadda jigon APC ya rasu a otal a Abuja

Daily Trust ta ruwaito cewa ya rasu ne a ranar Juma’a, 27 ga Maris, bayan da aka yi zargin ya makale a cikin mahayar sama da ta lalace a otal din.

Da yake magana kan lamarin jiya, shugaban APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa Ginsau ya isa Abuja kwana daya kafin taron domin kama wa wakilan jihar dakunan hotal.

Doguwa ya ce sun fara shiga fargaba ne lokacin da aka rasa Ginsau a wajen taron ranar Juma’a, wanda hakan ya sa suka fara nemansa ruwa a jallo a fadin Abuja.

Daga karshe, sun je ofishin 'yan sanda na Utako inda aka sanar da su cewa akwai wani hatsari da ya faru a otal din Chida kuma wani mutum ya mutu, daga bisani suka tabbatar da gawarsa ce.

A yanzu haka an kai gawar marigayin domin gudanar da binciken musabbabin mutuwarsa, kuma ana jiran sakamakon binciken 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Amurka ta ci karo da cikas, Iran ta illata ta a yakinta da kasar Isra'ila

Bayani daga bangaren otal din

Duk da cewa manajar otal din, Princess Oluchi, ta ki cewa uffan saboda binciken da ake yi, wata majiya ta ce an kama dakuna 150 ne ga wakilan Kano, amma mutane sama da 1,000 ne suka bayyana.

Majiyar ta ce daya daga cikin mahaya ta lalace har aka bar ta a bude, amma bisa tsautsayi marigayin, wanda ya kama daki a hawa na uku, ya shiga cikinta da safiyar Juma'a ba tare da sanin kowa ba, inda mahayar ta yi kasa da shi.

Majiyar ta ce ba a gano gawar ba sai washegari lokacin da aka fara jin wari yana tashi a cikin otal din, sannan aka gudanar da bincike, in ji rahoton Sahara Reporters.

Tutar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Iyalan Abdulsalami Ginsau sun yi magana

A madadin iyalan marigayin, Hamza Haladu ya bayyana lamarin a matsayin abin kaduwa, inda ya ce Ginsau na cikin koshin lafiya da kuzari kafin tafiyarsa.

Ya kara da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta shiga cikin maganar, inda gwamna ya tabbatar wa iyalan cewa za a bi kadun lamarin domin gano gaskiya.

Kara karanta wannan

Watakila ADC ta gyara zama a Sokoto, Sanatan APC na tunanin sauya sheka

Za a binne marigayin a ranar Alhamis a birnin Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Hadimin gwamna da kansilolin APC sun mutu

A wani rahoton, kun ji cewa hadimin Gwamnan Kebbi da wasu kansiloli biyu sun rasa rayukansu a hanyar zuwa babban taron APC a Abuja.

A cewar sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kebbi, Yahaya Sarki, ya fitar, wadannan mutane uku sun mutu ne bayan wata mota ta kade su a bakin hanya.

Ya ce motar ta kade su ne yayin da suke kokarin tsallaka titi bayan motarsu ta tsaya a hanya a lokacin da suke kan hanya don halartar taron APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262