JNI Ta Fadi Adadin Musulman da aka Kashe a Harin Jihar Filato

JNI Ta Fadi Adadin Musulman da aka Kashe a Harin Jihar Filato

  • Rahotannin da suka fito daga kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) sun bayyana adadin Musulman da aka kashe a wani hari da aka kai a Filato
  • Hakan na zuwa ne bayan wasu 'yan ta'dda sun kai harin mai uwa da wabi kan jama'a da dare a jihar Filato, inda sama da mutum 20 suka mutu
  • A yanzu haka dai kungiyar JNI ta sanar da cewa akalla Musulmai 10 ne ba a san a ina suke ba tun bayan harin da aka kai kuma ana neman su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce Musulmi huɗu na cikin waɗanda aka kashe a harin da aka kai daren Lahadi a Anguwan Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Lamari ya girma: Sanatan Amurka ya bankado 'sirrin' wasu manyan Najeriya

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar a ranar Litinin cewa mutane 27 aka kashe yayin da da dama suka jikkata a mummunan harin.

Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang
Gwamnan Filato tare da 'yan sanda. Hoto: The Plateau State Government
Source: Facebook

Shaidun gani da ido sun shaida wa Premium Times cewa maharan da suka zo a kan babura sun kai farmaki yankin da misalin ƙarfe 7:30 na dare suna harbe-harbe.

Musulman da aka kashe a jihar Filato

A cikin wata sanarwa da sakatarenta Salim Umar ya sanya wa hannu, JNI ta ce ta tabbatar daga rahotanni da iyaye Musulmi suka bayar cewa 'yan uwansu ma suna cikin waɗanda harin ya rutsa da su.

“Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Plateau na baƙin cikin tabbatar da mutuwar Musulmi huɗu tare da ɓacewar wasu 10 sakamakon harin da aka kai Rukuba a Jos ta Arewa.
“Bayan cikakken bincike da rahotannin da muka samu daga al’ummar Musulmi, mun gano cewa an kashe Musulmi huɗu yayin da ba a san inda 10 suke ba.”

An samo gawar Musulmi a Filato

Ta ƙara da cewa an gano gawar waɗanda aka kashe a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), yayin da waɗanda suka ɓace ba a ji duriyarsu ba tun daga ranar Lahadi, wayoyinsu ma a kashe suke.

Kara karanta wannan

Iran ta kai hari mai muni Saudi, ta raunata sojojin Amurka da jirginsu

Punch ta wallafa cewa JNI ta ce an gano mutane biyu da ke karɓar magani a JUTH, kuma tana hulɗa da iyalan waɗanda abin ya shafa.

Taswirar jihar Filato
Taswirar jihar Filato a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ƙungiyar ta miƙa ta’aziyya ga iyalan dukkan waɗanda suka rasa rayukansu tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, tana kuma yaba wa ƙoƙarin gwamnati wajen shawo kan lamarin.

Bayanin iyalan wadanda aka kashe

Kabir Yusuf, wanda ya ce shi ne babban ɗan’uwa ga ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe, Abubakar Yusuf, ya ce an kashe ɗan’uwansa ne yayin da yake dawowa tare da abokinsa daga ƙauyen Fobur inda suka je sayen tumatir.

“A ranar Lahadi ya je Fobur da babur domin sayen tumatir. Yawanci suna zuwa gona, kuma a ranar ya tafi da N700,000 ya sayo tumatir.
“A hanyarsu ta dawowa ne aka kai musu hari a Rukuba, abokinsa da ke bayan babur ya ji rauni amma ya tsira,”

'Dan Amurka na yawo a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa jama'ar Najeriya sun fara korafi bayan ganin wani dan Amurka na jawo a kauyukan Filato da wasu jihohi.

Kara karanta wannan

Kotu ta wanke tsohuwar minista daga zargin satar N2.5bn bayan ta daidaita da gwamnati Najeriya

Mutane na korafi game da hakikanin abin da dan Amurkan, Alex Birbir ke yi a Najeriya, inda suka ce yana kokarn haddasa fitina tsakanin Musulmi da Kirista.

Hankulan jama'a sun tashi ne a daidai lokacin da aka hango shi a wani waje da aka kai hari a yankin Rukuba a Filato ranar Lahadi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng