El Rufa'i Ya Gurfana a Kotu ana Jimamin Rasuwar Mahaifiyarsa

El Rufa'i Ya Gurfana a Kotu ana Jimamin Rasuwar Mahaifiyarsa

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an hango tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i a gaban wata kotu a jihar bayan sakin shi da aka yi
  • Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta saki El-Rufa'i domin samun damar halartar jana'izar mahaifiyarsa da ta rasu a Masar
  • ICPC ta tsare tsohon gwamnan ne saboda wasu zarge-zargen da ke da alaka da kuɗi kwanaki kadan bayan dawowarsa Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya halarci zaman kotu a jihar da safiyar yau Talata, 31 ga Maris, 2026.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC) ta shigar da tuhume-tuhume daban-daban a kansa a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri: Cikin jimami, ISWAP ta sanar da mutuwar babban kwamandanta

Nasir El_rufa'i a kotu
Yadda Nasir El_rufa'i ke kokarin shiga kotu a Kaduna. Hoto: Uche Diala
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa a makon da ya gabata, an gurfanar da shi a gaban Mai shari’a Rilwan M. Aikawa kan tuhume-tuhume guda 10 da suka shafi zargin karkatar da kadarorin gwamnati da sauransu.

Nasir El-Rufa'i ya gurfana a gaban kotu

Rahotanni sun nuna cewa an kawo tsohon gwamna kotun Kaduna bayan shafe kwanaki yana hidimat jana'iza da jimamin rasuwar mahaifiyarsa.

Dama dai a zaman da ta yi a baya, kotun ta sanya ranar 31 ga Maris, 2026 domin sauraron bukatu da korafin da aka gabatar, ciki har da neman beli da tsohon gwamnan ya yi.

An hango Nasir El-Rufa'i a kotun sanye da babbar riga tare da wasu jami'an ICPC a gefen shi a wani bidiyo da Uche Diala ya wallafa a Facebook.

Dalilin sakin El-Rufa'i a baya

A ranar 27 ga Maris, 2026, hukumar ICPC ta saki El-Rufa'i bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Ummar El-Rufai a birnin Alkahira na ƙasar Masar.

Kara karanta wannan

Yadda El Rufa'i ya sauke Alkur'ani, ya karance littafai 10 a hannun ICPC

El-Rufa'i da wasu daga cikin 'yan uwansa sun samu damar halartar jana'izar a Abuja tare da cigaba da zaman makoki a gidan shi.

Nasir El-Rufa'i a kotun Kaduna
Lokacin da Nasir El-Rufa'i ya shiga kotun Kaduna. Hoto: Uche Diala.
Source: Facebook

Me El-Rufa'i ke tsammani a kotu?

A yau Talata, aka sake gurfanar da El-Rufa'i a gaban babbar kotun jihar Kaduna tare da Amadu Sule, bisa zarge-zarge da suka haɗa da cin zarafi, zamba, niyyar aikata zamba, da kuma fifita wasu ba bisa ka'ida ba, da sauransu.

Ana sa ran daga baya hukumar za ta kai Malam Nasir El-Rufa'i zuwa Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, inda za a saurari buƙatarsa ta bayar da beli.

Manya sun je jana'izar Umma El-Rufa'i

A wani labarin, mun kawo muku cewa manyan Najeriya da dama sun halarci jana'izar mahaifiyar malam Nasiru El-Rufa'i a Abuja.

Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, manyan 'yan jam'iyyar APC da ADC sun halarci sallar gawar Hajiya Umma El-Rufa'i.

A gefe kuma, attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote da malaman addinin Musulunci kamar Sheikh Isa Ali Pantami da sauransu sun hallara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng