Bayan Watsi da Taron Abba, Sanata Kawu Sumaila Ya Sa Labule da Manyan APC

Bayan Watsi da Taron Abba, Sanata Kawu Sumaila Ya Sa Labule da Manyan APC

  • ‘Dan majalisar Kano ta Kudu ya kauracewa taron da gwamnan jiharsa, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kira domin duba muhimman batutuwa
  • Sanata Kawu Sumaila ya janye jikinsa daga wancan taro, inda ya gudanar da nasa taron tare da kiran jiga-jigan yan siyasa daga yankinsa
  • ‘Yan majalisar sun nuna damuwa kan abin da suka kira nuna wariya ga yankin Kano ta Kudu a lokacin da ake sauya siyasa a jihar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – ‘Yan majalisar wakilai daga yankin Kano ta Kudu sun gudanar da abin da suka kira muhimmin taro a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, 2026.

Sun zauna ne domin tattauna makomar siyasarsu, yayin da suke bayyana rashin jin dadinsu game da jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, manyan wakilan jam'iyyar 3 sun mutu a hatsarin mota

Sanata Kawu Sumaila ya ki halartar taron Abba
Sanata Kawu Sumaila tare da Abba Kabir Yusuf Hoto: Sen. S A Kawu Sumaila, Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A labarin da ya kebanta ga Daily Nigerian, taron da aka yi a Abuja ya samu jagorancin Sanata Kawu Sumaila.

Yan majalisar Kano sun yi taro

Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun haɗa da manyan ‘yan majalisar wakilai kamar Alhassan Doguwa, Kabiru Rurum, Abdulmumin Jibrin da Abdullahi Rogo.

Rahotanni sun nuna cewa taron ya zo ne kwana guda bayan da Sanata Sumaila da Kabiru Rurum suka kaurace wa gayyatar da gwamnan ya yi masu.

Su Kawu Sumaila za su gana da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Rahotanni sun ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kira su ne domin halartar wani babban taro da ‘yan jam’iyyar APC na majalisar dokokin jiha da ta ƙasa.

Wannan lamari na nuna ƙarin rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar a jihar Kano musamman bayan sauya shekar Gwamna.

Abin da 'yan majalisar Kano suka tattauna

Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan majalisar sun tattauna sosai kan makomar siyasarsu, inda suka koka da abin da suka kira rashin kulawar siyasa ga yankin Kano ta Kudu daga gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Kotu ta wanke tsohuwar minista daga zargin satar N2.5bn bayan ta daidaita da gwamnati Najeriya

Sun bayyana cewa ana yanke muhimman shawarwari da suka shafi yankin ba tare da cikakkiyar tuntubar wakilan yankin ba, lamarin da ke ƙara haifar da rashin gamsuwa a tsakaninsu.

Wata majiya ta ce ‘yan majalisar suna ci gaba da tuntubar tsofaffi da kuma masu rike da mukaman siyasa daga yankin, daga ciki har da wasu tsofaffin shugabannin jam’iyya.

A cewar majiyar, suna kuma neman shawarwari daga manyan ‘yan kasuwa, malamai da sauran masu ruwa da tsaki domin tsara sabuwar alkiblar siyasa ga yankin Kano ta Kudu.

Sai dai wata majiya ta daban ta bayyana cewa ana sa ran ‘yan majalisar da ke nuna rashin jin daɗin za su gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf a daren Litinin domin gabatar masa da bukatunsu.

Kano ba ta Kwankwasiyya ba ce - Kawu Sumaila

A baya, mun wallafa cewa yayin da rigimar jam'iyyar NNPP ke kara ƙamari, Sanata Kawu Sumaila ya yi magana inda ya shawarci Gwamna Abba Kabir.

Sanata Kawu Sumaila da ke wakiltar Kano ta Kudu ya ce ya kamata Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sani ba iya yan Kwankwasiyya ba ne kaɗai a jihar Kano.

Sanata Kawu Sumaila ya ce babban cin amana shi ne bijirewa Allah da ya yi masa gata a rayuwarsa inda ya ba shi shawara kan mulki na jagorantar al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng