Kwamishina da Hadimin Gwamna Radda Sun Yi Murabus, an Ji Dalilinsu
- Wasu daga cikin masu rike da mukamai a gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Dikko Umaru Radda sun yi murabus daga mukamansu
- Kwamishinan muhalli na jihar Katsina, Hamza Suleiman, na daga cikin mutanen da suka hakura da mukamnsu
- Hamza Suleiman ya nuna godiyarsa ga Gwamna Dikko Umaru Radda saboda damar da ya ba shi ta yi wa jihar Katsina hidima
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Mambobi biyu na majalisar zartarwar Gwamna Dikko Radda a gwamnatin jihar Katsina sun yi murabus.
Mambobin sun yi murabus ne biyo bayan cikar wa'adin da aka ba masu riƙe da muƙaman siyasa na su yi murabus idan suna da burin tsayawa takara.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce kwamishinan muhalli, Hamza Suleiman, da mataimaki na musamman ga Gwamna Radda kan harkar miyagun kwayoyi da safarar mutane, Shehu Daura, sun miƙa takardun yin murabus ɗinsu ga gwamnati.

Kara karanta wannan
Gwamna Zulum ya rusa majalisar zartarwa, ya kori dukkan kwamishinonin jihar Borno
Meyasa suka yi murabus?
Bincike ya nuna cewa mutanen biyun suna shirin tsayawa takarar neman kujerar sanata ne a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
Hamza Suleiman zai fafata ne wajen neman wakiltar shiyyar Katsina ta Kudu (Funtua) wadda a halin yanzu wani mamba na APC, Sanata Muntari Mohammed, ke kai.
Shi kuma Shehu Daura zai fafata ne da Sanata Nasiru Sani na APC, wanda ke wakiltar shiyyar Katsina ta Arewa (Daura).
Yayin da yake yi wa manema labarai bayani jim kaɗan bayan miƙa takardar murabus ɗinsa ga sakataren gwamnatin jiha (SSG), Bar. Abdullahi Faskari (wanda wani jami'i ya wakilta), Hamza ya nuna godiyarsa ga Gwamna Radda bisa ba shi damar yi wa jihar hidima.
Kwamishina zai yi takarar Sanata
Ya ce ya yi murabus ne domin ya tsaya takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC don neman kujerar sanata.
“Ina yin murabus ne domin na tsaya takarar sanata a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar mu, kuma ina yin hakan ne sakamakon kiran da mutanen shiyyar mu suka yi mini."
"Ina son shaida wa duk wanda yake saurare cewa biyayya ta ga Gwamna Dikko Radda ba za ta girgiza ba, saboda haka a shirye nake koyaushe na bi umarninsa."
- Hamza Suleiman

Source: Facebook
Gwamna Radda ya samu yabo
Ya yaba wa Gwamna Radda bisa jajircewarsa kan manufar "Build Your Future", jaridar Daily Trust ta kawo rahoton.
Hamza ya nuna kwarin gwiwar cewa kyawawan manufofin gwamnatin Radda za su ƙara samar da sakamako mai kyau idan aka sake zaɓen sa a shekara mai zuwa.
Ministan Shugaba Tinubu ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa adadin yawan ministocin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ragu biyo bayan murabus din daya daga cikinsu.
Karamin Ministan harkokin jin Kai da rage talauci, Yusuf Tanko Sununu, ya sanar da murabus dinsa daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa, Yusuf Sununu, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, wanda ya wakilci mazabar Shanga/Yauri/Ngaski, na shirin tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu a zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
