Hakulan Jama'a Sun Tashi a Wani Yanki na Birnin Abuja da Aka Fara Ruwan Sama
- Mazauna Ubosharu dake yankin Kwali sun bayyana fargaba kan yadda rufin asibitinsu yake yoyo yayin da aka fara kakar ruwan sama
- Rashin kayan aiki da magunguna ya tilasta wa masu juna biyu tafiya zuwa Abaji ko Kwali domin neman lafiya a kan babura
- Shugabannin yankin sun koka kan rashin ruwa mai tsafta, inda suka bukaci hukumar yankin da ta gina musu sabbin rijiyoyin burtsatse
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mazauna al'ummar Ubosharu dake gundumar Wako a ƙaramar hukumar Kwali a Abuja, sun bayyana matuƙar damuwarsu kan yanayin lalacewar babban asibitin yankin nasu.
Mazauna yankin sun ce fargabarsu ta ƙaru ne biyo bayan fara kakar ruwan sama, inda rufin asibitin yake yoyo sosai sakamakon iskar da ta kwashe sassan rufin kwanan kwanan nan.

Source: Getty Images
Abuja: Matsalar da Ubosharu ke fuskanta
Wani mazaunin yankin, Ismaila Danjuma, ya bayyana wa jaridar Daily Trust cewa
"Matsalar da asibitin nan yake fuskanta ya zama abin kunya sosai, rufin asibitin yana zubar da ruwa, neman magani a nan ya zama babban ƙalubale ga kowa."
Baya ga lalacewar ginin, mazauna yankin sun koka kan rashin magunguna a asibitin, inda aka tilasta musu tafiya zuwa Abaji ko Kwali domin sayen kwayoyin da ma'aikatan asibitin suka rubuta musu.
Yakubu Gambo, wanda matarsa ta haihu kwanan nan, ya bayyana cewa:
"Lokacin da naƙuda ta kama matata makonni biyu da suka gabata, sai dai na ɗauke ta a kan babur da daddare zuwa babban asibitin Abaji inda ta haihu, don ba za a iya karbar haihuwar a nan Ubosharu ba."
Ya ƙara da cewa duka ɗakunan jinya na maza da mata a Ubosharu suna yoyo, wanda hakan ke jefa marasa lafiya cikin mawuyacin hali idan ana ruwan sama a yankin .
Ana zargin gwamnati ta yi watsi da Ubosharu
Shugaban al'ummar yankin, Joshua Audu Gimba, ya bayyana takaicinsa kan yadda gwamnati ta yi watsi da asibitin duk da kusancinsa da babban titin Abuja zuwa Lokoja.
Ya bayyana cewa:
"Kamar yadda ku ke gani, asibitin yana da nisan mita kaɗan ne daga babban titi, kuma ana kawo waɗanda hatsari ya rutsa da su nan, amma sai a tura su Abaji don rashin kayan aiki."
Wannan yanayi yana nuna cewa asibitin wanda aka gina shi sama da shekaru 18 da suka gabata, yana buƙatar garambawul cikin gaggawa domin ya dace da buƙatun karuwar jama'ar yankin.

Source: Getty Images
Ƙalubalen rashin ruwa mai tsafta
Baya ga matsalar asibiti, al'ummar Ubosharu dake ƙaruwa kullum tana dogara ne kawai kan rijiyoyin burtsatse guda biyu waɗanda ba su wadatar da kowa.
Gimba ya ƙara da cewa:
"Mata suna tafiya mai nisa domin ɗebo ruwa a rafi, ko kuma su dogara da famfon dake kusa da tashar NNPCL saboda rashin isasshen ruwan famfo a yankinmu."
Al'ummar garin sun yi kira ga mahukuntan ƙaramar hukumar Kwali da su hanzarta gina musu ƙarin rijiyoyin burtsatse domin rage wa mata da yara wahalar tafiya neman ruwa.
Halin da marasa lafiya suka shiga a yajin- aiki
A wani labari, mun ruwaito cewa, an ji yadda marasa lafiya dake neman magani a kananu da manyan asibitocin gwamnati a Abuja suka shiga mawuyacin hali a kwanan baya.
Wannan kuwa ya faru ne sakamakon fadada yajin aikin da mambobin hadakar kungiyoyin ma’aikatan babban birnin tarayya (JUAC) suka yi a watan Janairu, 2026.
A lokacin yajin aikin, bincike ya nuna cewa asibitoci da dama sun kasance tamkar kufai, inda aka ga 'yan tsirarun marasa lafiya suna jiran tsawon sa'o'i ba tare da ganin likita ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


