Rahoto: Yadda Yakin Iran da Amurka Ya Shafi Tattalin Arziki da Tsaron Najeriya

Rahoto: Yadda Yakin Iran da Amurka Ya Shafi Tattalin Arziki da Tsaron Najeriya

Abuja - Yayin da yaƙin da ake fafatawa tsakanin ƙasar Amurka da Iran ya shiga kwana na 30, duniya ta tsinci kanta a cikin wani babban sauyi na tattalin arziƙi da tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ga Najeriya, wannan rikici ya zama tamkar "takobi mai kaifi biyu" – yana kawo maƙudan kuɗi ta kofa ɗaya, yayin da yake kwashe albarkar talaka ta wata kofar.

Yakin Amurka/Isra'ila da Iran: Abubuwan da suka faru a Najeriya cikin kwana 30
Shugaba Bola Tinubu (hagu), da bakin hayaki ya tashi a Beirut (tsakiya) da hada-hadar ababen hawa a titin Legas. Hoto: @officialABAT/X, IBRAHIM AMRO and Frédéric Soltan via Getty Images
Source: Getty Images

Wannan yaƙi, wanda ya ɓalle a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, bayan da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da gagarumin harin sararin samaniya mai taken "Operation Epic Fury", ya bar baya da ƙura, in ji rahoton The Sun.

Mafarin yaƙin: Kisan Khamenei da rufe Hormuz

Rahoton Aljazeera ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga shekaru na takun-saƙa kan shirin nukiliyar Iran.

Kara karanta wannan

Tinubu ya cika shekaru 74 a duniya, ya aika muhimmin sako ga 'yan Najeriya

Sai dai, al'amura sun rincabewa ne a farkon wannan shekara ta 2026 lokacin da gwamnatin Trump ta haɗa gwiwa da Isra'ila wajen kai hare-hare sama da 900 cikin sa'o'i 12 kan Iran.

Wannan harin ya yi sanadin kisan babban jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, da sauran manyan jami’an ƙasar, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.

A matsayin ramuwar gayya, Iran ta rufe mashigar ruwan Hormuz, wanda shi ne babban hanyar da kashi 20% na man fetur ɗin duniya da kashi 25% na iskar gas (LNG) ke bi.

Wannan mataki ya janyo tashin farashin ɗanyen mai zuwa tsakanin $90 zuwa $114 kowace ganga, lamarin da ya tsorata ƙasashen Turai da Asiya amma ya ba Najeriya wata dama ta daban.

Yadda yakin Iran da Amurka ya shafi Najeriya

1. Tattalin arziƙi

A matsayin ƙasa mai fitar da mai (OPEC), wannan yaƙi ya zamar Najeriya tamkar damina a lokacin rani ta fuskar samun kuɗin shiga.

Tunda man fetur ɗin Najeriya ba ya bi ta mashigar Hormuz, kasar na samun damar sayar da mai zuwa Turai da Amurka ba tare da fuskantar wani cikas ba.

Kara karanta wannan

Pakistan ta gana da Iran, an taɓo batun sulhu da Amurka

Saboda wannan dalili, Najeriya ta samu akalla tagomashi uku:

  • Rarar kuɗi: Masana tattalin arziƙi sun yi hasashen cewa idan yaƙin ya ci gaba da dorewa, Najeriya na iya samun rarar kuɗi tsakanin N2.3trn zuwa N30.2trn, in ji rahoton Vanguard.
  • Asusun kasa: Ma'ajiyar kuɗin waje ta haura $50bn, wanda hakan ya ba gwamnati damar kare darajar Naira da kuma rage raɗadin bashi a kasuwar duniya.
  • Matatun cikin gida: Matatar Dangote ta samu ƙarin tagomashi domin sarrafa ɗanyen mai a cikin gida maimakon dogaro da taceccen mai daga yankin Gabas ta Tsakiya da yaƙi ya shafa.

2. Tsadar fetur da hauhawar farashi

Yakin Iran da Amurka ya jawo hauhawar farashin fetur da na kayayyaki.
Masu ababen hawa na kokarin sayen fetur a gidan man NNPCL da ke Legas. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Duk da waɗannan biliyoyin nairori da ke shigowa asusun gwamnati, ɗan Najeriya da ke neman abincin yau da gobe yana cikin garari sakamkon wannan yaki, cewar rahoton Punch.

Dalili kuwa shi ne Najeriya har yanzu tana shigo da taceccen mai daga waje, wanda farashinsa ke tashi daidai da na ɗanyen mai.

Uwa uba, ita ma matatar man Dangote tana karawa da rage farashin fetur din ne gwargwadon yadda farashin danyen mai yake a duniya, don tana shigo da wani man daga waje.

Kara karanta wannan

Yaki zai fadada: Kasar Afrika 1 tilo ta fito za ta taya Isra'ila yakar Iran

A halin da ake ciki a Najeriya:

  • Farashin fetur: Litar fetur wadda take kusan N1,036 a watan Janairu, yanzu ta haura N1,400 a wasu sassan ƙasar a wannan watan Maris, in ji rahoton Daily Trust.
  • Hauhawar farashin kayayyaki: Masana daga ƙungiyar NESG sun yi gargaɗin cewa za a iya samun ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki da 1.3% zuwa 5.2%, wanda zai kara farashin abinci da sufuri. Ana fargabar matakin hauhawar farashin kaya zai kai 30% zuwa 35% kafin ƙarshen watan Afrilu.

3. Tsaro

Wannan yaƙi ya rura wutar adawa a cikin gida, musamman a Arewacin Najeriya inda mabiya ɓangaren Shi'a (IMN) suke da rinjaye.

'Yan Shi'a sun gudanar da zanga zanga bayan kisan Ayotallah Khamenei
Wasu 'yan Shi'a na zanga zanga a Najeriya. Hoto: Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Bayan kisan jagoran addinin Iran, Legit Hausa ta ruwaito cewa, 'yan Shi'a sun gudanar da tattaki a manyan biranen kasar nan kamar Kano, Kaduna, Bauchi, Gombe da Abuja da sauransu.

Jim kadan bayan haka, ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya fitar da sanarwar gargaɗi ga ma'aikatansu a shafinsa na intanet, inda ya nuna fargabar cewa zanga-zangar IMN na iya rikida ta zama hare-hare ga Amurka a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zo ku nema: Gwamnati ta bude shafin shirin tallafa wa ƴan Najeriya miliyan 10

Rundunar 'yan sanda da sojoji sun ƙarfafa tsaro a manyan ofisoshi da sansanonin dake fadin ƙasar domin guje wa ɓallewar rikici, kamar yadda rahoton Arise News ya nuna.

4. Matsayar Najeriya kan yakin Iran

Gwamnatin Najeriya ta bukaci kasashen duniya da su nuna taka tsan-tsan tare da amfani da tattaunawa domin kwantar da tarzomar dake faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana cewa Najeriya ba za ta mara wa kowane bangare baya ba a rikicin Iran da su Amurka, in ji rahoton The Nation.

Najeriya ta ba da fifiko wajen tabbatar da tsaron 'yan kasar dake zaune a kasashen waje yayin da take kira ga zaman lafiya.

Gwamnati ta bayyana cewa tana sanya ido sosai kan yadda al'amura ke sauyawa domin tabbatar da cewa 'yan ƙasar ba su faɗa cikin haɗari ba

Sai dai, wasu masana kamar Femi Falana sun yi kira ga gwamnati da ta haɗa kai da ƙasashe irin su Rasha da China domin takawa Amurka burki kan hare-haren da take kaiwa, in ji rahoton Channels TV.

Najeriya ta dauki matakai kan yakin Iran

Kara karanta wannan

Babbar magana: Netanyahu ya shirya kawo matsala ga Trump kan yaki da Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta dauki wasu muhimman matakai tun bayan fara yakin Iran da Amurka/isra'ila a ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Bayan fara yakin Iran, gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan Najeriya da ke zaune a Iran da ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

Yayin da yakin ya jefa duniya cikin matsalar makamashi, inda gas, fetur, man jirgin sama da sauransu suka tashi, Najeriya ta ce tana shirye ta warware matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com