An Rage Mugun Iri: ISWAP cikin Jimami Ta Sanar da Mutuwar Babban Kwamandanta
- Kungiyar ISWAP ta sanar da mutuwar babban kwamandanta wanda ke cikin majalisar 'Shura' na kungiyar wanda yake da tasiri
- ISWAP ta tabbatar da mutuwar Abu Yahya Al-Muhajir, tana mai bayyana hakan a matsayin babbar asara
- Rahotanni sun nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama yayin harin Malam Fatori da sojoji suka dakile
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Kungiyar ISWAP a jihar Borno tana cikin jimami bayan tabbatar da mutuwar babban kwamandanta.
Kungiyar ISWAP ta tabbatar da mutuwar wani fitaccen mambanta a majalisar Shura, Abu Yahya Al-Muhajir.

Source: Original
A cikin wata sanarwa da Zagazola Makama ta samu, ISWAP ta yi jimamin rasuwar tare da yabon rawar da ya taka a kungiyar.
Yadda bam ya kashe mutane a azumi
Wannan kyakkyawan labari na zuwa ne bayan yan ta'addar Boko Haram sun dasa bama-bamai a Borno wanda ya jikkata mutane da dama.
Bayan mako biyu da kai mummunan harin kunar bakin wake birnin Maiduguri da ke jihar Borno, an fara samun bayanai kan yadda aka tsara harin.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta yi amfani da wasu matasa a cikin Keke Napep domin kai hari wani asibiti a Maiduguri.
Wani jami'in da ke aiki a asibitin ya bayyana yadda suka yi kokarin hana matasan shiga asibitin da bama-baman da suka boye a kofin ajiye ruwan zafi.
Kungiyar ISWAP ta yi jimamin mutuwar kwamandanta
Kungiyar ta bayyana mutuwar tasa a matsayin daya daga cikin manyan asarorin da ta taba yi a ‘yan kwanakin nan a yankin Malam Fatori.
Majiyoyin tsaro sun ce ana zargin Al-Muhajir na da alaka da hare-haren baya-bayan nan a yankin Tafkin Chadi.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko an kashe shi ne yayin harin da kungiyar ta kai Malam Fatori wanda bai yi nasara ba, ko kuma a wani farmakin sama da aka kai daga baya.

Source: Twitter
Ana zargin harin sojojin ya raunata Al-Muhajir
Rahotanni sun nuna cewa sojojin Najeriya sun dakile harin, inda aka kashe kimanin ‘yan ta’adda 80 yayin artabu da kuma farmakin da ya biyo baya.
Majiyoyin sun kara da cewa akwai yiwuwar Al-Muhajir ya samu munanan raunuka a harin, wanda daga bisani ya yi ajalinsa.
Wani rahoto ya nuna cewa harin da aka kai ranar 18 ga Maris, 2026 ya yi sanadin mutuwar kimanin ‘yan kungiyar 84 tare da jikkata wasu da dama.
Sojoji sun kashe Boko Haram 100 a Borno
A baya, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan Boko Haram yayin da suka yi musayar wuta a jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun shirya kai wani mummunan hari ne a daidai lokacin da aka fara shirye-shiryen bikin sallah a jihar.
Sojojin Najeriya sun fitar da sunayen wasu daga cikin manyan 'yan ta'addan da aka tabbatar da kashe su har lahira yayin farmakinda aka kai.
Asali: Legit.ng

