Iran Ta ba Amurka, Isra’ila Wa’adi bayan Hari a Jami’a, Ta Fadi Illar da Za Ta Masu
- Dakarun 'Islamic Revolutionary Guard Corps' a Iran watau IRGC ta yi gagarumar barazana ga Amurka da Isra'ila a yakin da ake yi
- IRGC ta yi barazanar kai hari kan jami’o’in Amurka a Gabas ta Tsakiya bayan hare-haren da suka lalata wasu jami’o’i a Iran
- Ta bukaci Amurka ta yi Allah-wadai da harin kafin wa’adin da aka sanya, tare da gargadin ma’aikata da dalibai su guji kusantar harabar jami’o’i
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Rundunar 'Islamic Revolutionary Guard Corps' ta Iran ta yi barazanar kai hari kan jami’o’in Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Hakan na zuwa ne bayan da ta zargi hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila da lalata wasu jami’o’i biyu a Iran.

Source: Facebook
A wata sanarwa da CBS News ta samu, rundunar ta bukaci gwamnatin Amurka ta fito fili ta yi Allah-wadai da harin kafin karfe 12 na rana ranar Litinin, 30 ga Maris.
Rundunar IRGC ta illata Amurka da Isra'ila
Rundunar tsaro ta IRGC da ke kasar Iran ta bayyana nasarar da ta samu yayin da ake ci gaba da yaki a Gabs ta Tsakiya.
IRGC ta ce ta lalata bama-bamai 120 a yankin Fars wadanda aka jefa yayin hare-haren Amurka da Isra’ila kwanaki da suka gabata.
Rahoto ya ce an gano su a kauyen Kafri da wasu yankuna da ke kusa dauke da bama-baman wadanda ke da mugun hatsari.

Source: Getty Images
Gargadin da Iran ta yi ga Amurka, Isra'ila
Sanarwar ta kara da cewa idan ba a yi hakan ba, jami’o’in Amurka da ke yankin za su iya fuskantar martani, cewar Punch.
Ta kuma gargadi malamai, ma’aikata da dalibai na jami’o’in Amurka da ke yankin su nisanci harabar jami’o’in da tazarar kilomita daya domin tsaro.
Akwai jami’o’in Amurka da dama da ke da rassa a kasashen yankin Gulf, ciki har da Texas A&M University a Qatar da New York University a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren da aka kai daga daren Juma’a zuwa Asabar sun shafi Tehran, ciki har da jami’ar kimiyya da fasaha, inda aka samu lalacewar gine-gine.
Sai dai an ce ba a samu asarar rayuka ba sakamakon harin da aka kai wanda ya jawo maganganu game da yakin da ake yi.
Amurka ta magantu kan karkare yakin Iran
An ji cewa kasar Amurka ta yi magana game da nasarorin da samu yayin yakin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Amurka ta ce ta cimma yawancin burinta a yakin Iran, amma za ta ci gaba da kai hare-hare na ɗan lokaci domin ganin bayan gwamnatin Iran.
Mataimakin shugaban Amurka ya ce farashin mai ya tashi sakamakon rikicin, amma ya tabbatar da cewa hakan na wucin gadi ne.
Asali: Legit.ng

