Bayan Kisan Sarki a Fada, Wani Basarake na Kwance a Asibiti da Aka Kai Masa Hari

Bayan Kisan Sarki a Fada, Wani Basarake na Kwance a Asibiti da Aka Kai Masa Hari

  • Wani mutum ya ba mutane mamaki matuka bayan kai wa basarake hari har cikin fadarsa wanda ya tayar da hankula
  • Sarkin Ogbagi a Ondo, Oba Victor Adetona, ya jikkata bayan kai masa hari a cikin fadarsa da ke karamar hukuma Akoko ta Arewa maso Yamma
  • Lamarin ya tayar da hankula musamman bayan kisan wani Sarki a Agamo kwanan nan, yayin da wanda ake zargi ya kai hari bayan neman aikin direba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Akoko, Ondo - Wani Sarki mai daraja ta daya a jihar Ondo, Owa na Ogbagi ya jikkata bayan kai masa hari har cikin fadarsa.

Basaraken mai suna Oba Victor Olasehinde Adetona, ya gamu da tsauysayin ne bayan wani mutum ya kai masa hari a fada.

An farmaki wani Sarki har cikin fadarsa a Ondo
Taswirar jihar Ondo da aka kai wa Sarki hari har fada. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahotanni daga Vanguard sun ce lamarin ya faru ne a yankin Akoko ta Arewa maso Yamma, inda wanda ake zargi mai suna Tope Adelani ya shiga fadar da misalin karfe 11:00 na safe.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, manyan wakilan jam'iyyar 3 sun mutu a hatsarin mota

An farmaki Sarki har cikin fadarsa

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa Adelani ya kai hari ga Sarkin, inda ya jikkata shi sosai kafin a garzaya da shi wani asibiti mai zaman kansa domin samun kulawa.

Majiyoyi sun ce wanda ake zargin ya kasance mai yawan zuwa fadar, kuma ya je wajen Sarkin domin neman aikin direba amma aka ce babu gurbi.

An ce bayan ganawar, Sarkin ya fita gonarsa, ya bar Adelani a fadar, amma rikici ya barke ne bayan dawowarsa daga gonar.

Rahotanni sun ce Adelani ya bi Sarkin zuwa cikin fada, ya kwace wayoyinsa tare da kashe su kafin daga bisani ya kai masa hari.

An cafke matashi da ya farmaki Sarki a fadarsa
Basarake a Ondo, Victor Olasehinde Adetona da matashin da ya kai masa hari a fada. Hoto: Ogbagi Eagles' Watch.
Source: Facebook

Yadda aka cafke matashi da ya farmaki Sarki

Iyalan Sarkin da suka yi kokarin shiga tsakani suma sun samu raunuka yayin da lamarin ya rikide zuwa fada mai tsanani.

Daga baya jami’an tsaron fada sun yi nasarar cafke wanda ake zargin tare da mika shi ga hukumomi bayan sun kwato wuka a hannunsa.

Kara karanta wannan

Komai ya fito: Yadda Boko Haram ta saki bama bamai kan masu azumi a Borno

Matasan Ogbagi sun yi tir da harin, suna mai cewa abin ya saba wa al’adu da darajar mutanen yankin, tare da bayyana goyon bayansu ga Sarkin.

Sun kuma bukaci mazauna yankin su kwantar da hankula, su guji daukar doka a hannu, tare da kira ga gwamnati ta kara tsaro a fadar Sarkin.

Martanin yan sanda game da harin

Wakilin Legit Hausa ya tuntubi kakakin rundunar yan sanda a jihar, DSP Jimoh Abayomi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai Abayomi ya ce har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a kai korafin abin da ya faru da hukumarsu ta yan sanda ba sai dai ofishin NSCDC.

An kashe Sarki a fadarsa a Ondo

A baya, an ji cewa wasu mahara su shida sun yi garkuwa da Oba Kehinde Jacob Falodun sannan suka kashe shi a kusa da fadarsa da ke a jihar Ondo.

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi amfani da karfin tuwo wajen fitar da Sarkin daga fadarsa kafin su harbe shi.

Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin, sannan ta bayyana matakan da aka dauka zuwa wannan lokaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.