Komai Ya Fito: Yadda Boko Haram Ta Saki Bama Bamai kan Masu Azumi a Borno
- Bayan mako biyu da kai mummunan harin kunar bakin wake birnin Maiduguri da ke jihar Borno, an fara samun bayanai kan yadda aka tsara harin
- Wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta yi amfani da wasu matasa a cikin Keke Napep domin kai hari wani asibiti a Maiduguri
- Wani jami'in da ke aiki a asibitin ya bayyana yadda suka yi kokarin hana matasan shiga asibitin da bama-baman da suka boye a kofin ajiye ruwan zafi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Sababbin bayanai sun bayyana kan yadda wasu matasa uku da ake zargi sun yi yunkurin tarwatsa sassan asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri da bam da suka boye a cikin kofin ajiye ruwan zafi.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda ake zargin ‘yan kunar bakin wake ne sun nufi babban ginin asibitin domin jawo mummunan hari kan marasa lafiya da masu ziyara, wanda zai iya zama daya daga cikin mafi muni a ‘yan kwanakin nan.

Source: Facebook
Wani rahoto na Musamman da Punch ta hada ya nuna cewa ba a ba su damar shiga ba, lamarin da ya kai ga fashewar bama-baman a kofar asibitin a ranar 16 ga Maris, 2026.
Yadda Boko Haram ta saki bam a Borno
Wani jami’in tsaron asibitin, Ali Musa, ya bayyana maharan a matsayin matasa masu kananan shekaru da suka yi kokarin ketare dokokin tsaro domin shigar da bam din cikin asibitin.
A cewarsa, wasu matasa “jikinsu duk datti” sun isa kofar asibitin ne a cikin Keke Napep, dauke da kofin ajiye ruwan zafi kamar yadda ‘yan uwa ke kawo wa marasa lafiya abinci da ruwa.
Ya kara da cewa:
“Mun ji labarin fashewar bam a cikin gari, nan take muka tsaurara tsaro a wajenmu. Mu biyu ne kawai a bakin aiki a lokacin, sauran sun je buda baki."
'Bayan wani lokaci, sai ga su sun zo da gudu suna kokarin karya dokar shiga asibitin."
“Su uku ne — matasa biyu da direban keken. Ina ganin shekarunsu kusan 13 ko 14. Sun yi kama da marasa tsafta. Na yi zargin akwai matsala saboda yadda suka shigo.
“A al’ada, duk wanda ya zo dole ne ya rage gudu domin a duba shi. Amma su sun shigo da gudu sosai. Nan na gane akwai matsala, sai na tsayar da su na ce su koma baya. Da farko sun ki, daga baya suka juya,”
Inji shi.

Source: Original
Yadda aka jefa bam a Borno
Jami'in tsaron asibitin ya kara da cewa daya daga matasan da ke cikin Keke Napep ya jefa masa kofin da ke hannunsu yayin da suke komawa baya.
“Yayin da suke ja da baya, daya daga cikinsu ya jefa mani kofin. Na harba shi da kafa, ya fadi. Sai na ji wani kara mai karfi ya tashi, nan take na kwanta a kasa. Na ji rauni a hannu.
“Bayan fashewar, na yi kokarin zuwa wajen abokiyar aikina domin duba ta, amma na samu kafarta ta karye. Na kuma ga wani almajiri a kwance a kasa.
“Bayan na ja matar daga wurin, wani bam ya sake fashewa kusa da mu, sai na tsallaka cikin lambu. Duka kafafuna sun samu rauni,”
Inji shi.
China da Najeriya sun hada kai
A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta yi wani taro na musamman da dakarun kasar China a birnin tarayya Abuja.
Rundunar sojin saman Najeriya, ta bayyana cewa za ta yi hadaka da China domin karfafa dakarunta da dabarun yaki domin magance matsalolin tsaro.
Taron ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalolin tsaro da suka hada da na 'yan ta'addan Boko Haram da 'yan bindiga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


