Kotu Ta Wanke Tsohuwar Minista daga Zargin Satar N2.5bn bayan Ta Daidaita da Gwamnatin Najeriya
- Kotu ta wanke tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah, daga zargin damfara bayan sulhu da gwamnati
- An zargi tsohuwar minista a zamanin Shugaba Goodluck Jonathan da almundahanar kudin da yawansu ya haura Naira biliyan 2.5
- Sai dai kamfanoni biyu da ke da alaƙa da lamarin sun amsa laifi tare da biyan diyya ga gwamnatin Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja– Babbar kotun babban birnin tarayya da ke Maitama a Abuja ta lashe zargin tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah, da handame dukiyar kasa.
An zargi Stella Oduah da handame kudin Najeriya tare da wadansu da aka yi zargin da su aka yi harkar.

Source: Twitter
Premium Times ta wallafa cewa amma an samu nasarar cimma yarjejeniya tsakaninta da gwamnatin Najeriya.
Stella Oduah ta mayar da kuɗin gwamnati
Jaridar The Cable ta wallafa cewa lauyan gwamnati, wanda ke kula da shari’o’in tarayya, ya shaida wa kotu cewa waɗanda ake tuhuma sun mayar da dukkanin kuɗin da ake zargin sun karɓa ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce ya samu umarni daga Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya da Ministan Shari’a na ƙasa, Lateef Fagbemi, domin sanar da kotu cewa gwamnati ta karɓi kuɗin da ake magana a kai.
Bayan wannan bayani, ya roƙi kotu da ta janye ƙarar da aka shigar a kansu, buƙatar da lauyoyin masu kare kansu suka goyi baya.
Kotu ta sallami shari'ar Stella Oduah
Alƙalin kotun, Hamza Mu’azu, ya amince da hakan, inda ya bayyana cewa an soke ƙarar tare da sallamar waɗanda ake tuhuma.
Sai dai wannan hukunci ya biyo bayan tattaunawar sulhu da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu, wanda ya jinkirta fara shari’ar tun bayan gurfanar da su a watan Disamban 2025.
Tun farko dai an tuhume su da damfarar kuɗi har Naira biliyan 2.5 daga ma’aikatar sufurin jiragen sama, da sunan gudanar da ayyukan tsaro da kula da fasaha.

Source: Twitter
Sai dai duk da hukuncin, kotu ta kama kamfanoni biyu da aka yi amfani da su wajen aikata laifin. Sun haɗa da Sobora International a Global Offshore Marine.
Dukkaninsu sun amsa laifin damfara tare da amincewa su biya diyya ga gwamnatin tarayya. Alƙalin kotun ya umarce su da su mayar da sama da Naira biliyan 1.2.
Haka kuma ya bayar da umarni, inda ƙwace wasu kuɗi da aka gano yayin binciken a kan hannu cikin wannan badakala.
An kai Stella Oduah kotu
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta gurfanar da tsohuwar Ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah a gaban babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja.
Wannan shi ne karo na biyu da gwamnati ta gurfanar da ita a gaban kotu kan tuhume-tuhumen da suka shafi karkatar da dukiyar kasa da suka kai biliyoyin Naira.
Alkalin kotun, Mai Shari'a Hamza Mu'azu ya bada belin Stella tare da kwace fasfo dinta domin ka da ta gudu ana cikin shari'a yayin da aka yi ƙoƙarin kwato dukiyar Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

