Wane Hali Sheikh Khalifa Zaria ke ciki? Iyalansa Sun Yi Karin Haske kan Lamarin

Wane Hali Sheikh Khalifa Zaria ke ciki? Iyalansa Sun Yi Karin Haske kan Lamarin

  • Iyalan Sheikh Sani Abdulkadir Khalifa Zariya sun yi karin haske kan halin da yake ciki tun bayan yada jita-jitar rasuwarsa
  • Ɗansa mai suna Ibrahim ya bayyana cewa an hana malamin ganawa da lauyoyi kuma hukumomi ba su ba su wani bayani ba kan binciken ba
  • Iyalan sun buƙaci gwamnatin Najeriya ta gurfanar da shi a kotu idan akwai zargi tare da ba su damar ganin mahaifinsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - A Najeriya, ana ta yada jita-jitar cewa Sheikh Sani Abdulkadir Khalifa Zaria ya rasu a hannun hukumomin kasar nan wasu zarge-zarge.

Hakan ya biyo bayan cafke malamin da aka yi kan zargin alaka da wani soja da ake tuhuma da hannu a yunkurin juyin mulki.

Iyalan Sheikh Khalifa Zaria sun magantu kan halin da yake ciki
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Khalifa Zariya. Hoto: Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir.
Source: Facebook

Iyalan Sheikh Khalifa Zaria sun koka

Kara karanta wannan

Gargadi mai tsauri da Trump ya yi ga kasar Iran kan sharudansa na zaman lafiya

Jaridar BBC Hausa ta tattauna da wasu daga cikin iyalan malamin game da halin da yake ciki a yanzu.

Daya daga cikin ƴaƴansa, Ibrahim Sani Khalifa ya ce har yanzu ba su san halin da mahaifinsu ke ciki ba.

Ibrahim ya ce an hana mahaifin nasu ganawa da lauyoyinsa kuma an hana ba da belinsa a baya wanda ya daga masu hankali.

Ya ce har yanzu hukumomi ba su ce masu komai ba sannan babu wani labari game da abin da suka gano game da binciken da suke yi.

Ya ce:

"Mu ma yadda mutane ke jin wannan labari, haka kawai mu ma muke ji, ba abin da jami'an tsaro suka ka ce mana kan haka,
"Mu ma mun dade ba mu gan shi ba, tun da aka cafke shi, a cikinmu ba wanda ya ƙara jin halin da yake ciki, ko jin duriyarsa, ba mu ji labarin wani da ya ce ya gan shi ba har yau. "
Ana jita-jitar Sheikh Khalifa Zaria ya rasu a hannu hukumomi
Taswirar jihar Kaduna da aka cafke malamin a watan Disambar 2025. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda hankulan iyalan malamin suka tashi

Kara karanta wannan

Ana rade radin Sheikh Khalifa Zariya ya rasu, Atiku ya yi magana

Ibrahim ya bayyana cewa suna cikin tashin hankali bayan fara ganin rade-radin rasuwar malamin, sai dai ya ce ba za su iya sanin gaskiyar labarin ba har zuwa yanzu, ya ce sun gaza samun karin bayanai daga hukumomin kasarkan haka.

"Wannan labari na mutuwa da ake yadawa dai ba za mu iya tabbatar da haka ko a'a ba. saboda ko an tambaye mu tabbaci, ba mu da ita."
"A hukumace ba a ba mu bayani cewa ba yana nan ba, ko ya rasu ko wani abu ya faru."

Iyalan malamin sun buƙaci gwamnatin Najeriya su gabatar da shi a gaban shari'a cewa idan akwai abin da ake zargin sa da shi domin hakan zai ba su damar sake ganin shi.

Atiku ya bukaci a saki Sheikh Khalifa Zaria

An ji labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, Atiku Abubakar ya fusata kan ci gaba da tsare malamin Musulunci, Sheikh Sani Abdulkadir Khalifa Zaria.

Atiku ya bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bayyana halin da malamin ke ciki tare da kira a sake shi ko gurfanar da shi a gaban kotu.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rade-radin cewa malamin ya rasu, inda wasu majiyoyi ke cewa yana nan da ran shi a tsare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.