"Babban Kuskuren da El Rufai Ya Tafka da Ya Dawo Najeriya," Dalung Ya Yi Bayani

"Babban Kuskuren da El Rufai Ya Tafka da Ya Dawo Najeriya," Dalung Ya Yi Bayani

  • Solomon Dalung ya bayyana cewa Nasir El-Rufai ya nuna dattako wajen mika kansa ga EFCC duk da cewa hakan ya zama babban kuskure
  • Ana tuhumar tsohon gwamnan Kaduna kan karkatar da kudaden sallama da suka kai Naira miliyan 579 da kuma boye wasu kudade
  • Tsohon ministan wasanni, Dalung ya yi ikirarin cewa shari'ar El-Rufai ba za ta je ko ina ba domin hukumomin Najeriya ba su da kwararan hujjoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tafka “babban kuskure.”

A cewar Solomon Dalung, miƙa kansa ga hukumomin tsaro kafin a gurfanar da shi a kotu, shi ne babban kuskuren da El-Rufai ya yi bayan dawowarsa Najeriya.

Solomon Dalung ya ce MAlam Nasir El-Rufai ya tafka kuskure da ya mika kansa ga hukumomin Najeriya.
Malam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna zaune a filin jirgin sama. Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

'Gwamnati na tsoron El-Rufai' - Dalung

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya sauke kwamishinansa a Kano, ya faɗi dalili n yin waje da shi

Dalung ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata hira da gidan talabijin na Trust TV, inda ya yi iƙirarin cewa gwamnati tana tsoron tsohon gwamnan ne sosai.

A cewar Dalung, tun farko gwamnati ta yi ƙoƙarin kama El-Rufai a filin jirgin sama amma hakan ya gamu da cikas, inda mutane suka hana a tafi da shi.

Tsohon ministan ya ce:

“Gwamnati na tsoron El-Rufai sosai, suna tunanin har aka bar shi yana yawo a gari to zai iya iya kulla masu wani abu, don haka suke son ci gaba da tsare shi.
"Sun yi ƙoƙarin kama shi tun a filin jirgi amma hakan ya faskara, a nan ne suka gane cewa kama shi ta karfi zai iya haifar da tarzoma.”

Kuskuren El-Rufai da rusa shirin gwamnati

Duk da cewa Dalung ya kira miƙa kan da El-Rufai ya yi a matsayin kuskure, ya kuma bayyana cewa hakan ma ya zama wani tarko da El-Rufai ya dana wa gwamnatin.

Ya ce:

“Abin da ya yi shi ne ya nuna girma da sanin ya kamata, kuma sun faɗa tarkonsa domin miƙa kansa da wuri ya hana su damar kitsa wani abu a tuhume-tuhumensa.”

Kara karanta wannan

El Rufa'i na iya samun cikas, kotu ta gano babban kuskure a kararsa kan ICPC

Dalung ya ƙara da cewa:

“Don haka, sun tsare shi amma ba su da tuhumar da za su yi masa, kuma ba su da wani laifi da za su ce ya aikata a ƙasa. Don haka suka fara neman ko wadanne irin laifuffuka da za su ɗora masa.”

Ya jaddada cewa shari’ar El-Rufai ba za ta je ko’ina ba domin an gina harsashinta ne a kan son rai ba a kan doka ba.

Hukumar ICPC ta gurfanar da El-Rufai a kotu kan tuhume tuhume da suka shafi halatta kudaden haram.
Malam Nasir El-Rufai (farko daga dama) a cikin babbar kotun tarayya da ke Kaduna ranar da ICPC ta gurfanar da shi. Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

Tuhumar da ake yi wa El-Rufai

Hukumar yaƙi da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) da kuma takwararta ta ICPC ne suka riƙa musayar tsare tsohon gwamnan tun a ranar 18 ga watan Fabrairu.

A ranar Talata aka gurfanar da shi a gaban kotu kan zarge-zargen da suka shafi kari a kan kuɗaɗen sallama da suka kai Naira miliyan 579.7 da adana maƙudan daloli da suka kai $817,900 a asusun bankinsa na tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Awanni da raka mahaifinsa kotu, Bello El-Rufai ya ziyarci babban dan siyasa a Kaduna

A halin yanzu, ‘yan Najeriya suna zuba ido su ga yadda wannan takaddama tsakanin tsohon gwamnan da hukumomin yaƙi da cin hanci za ta ƙare, musamman duba da kalaman Dalung waɗanda suka nuna cewa shari'ar tana da nasaba da siyasa.

Kalli hirar Solomon Dalung a nan kasa:

Rahoton zaman farko na shari'ar El-Rufai

Tun da fari, mun ruwaito cewa, babbar Kotun Tarayya ta ɗage sauraron buƙatar neman belin tsohon gwamna, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 31 ga watan Maris, 2026.

Lauyan El-Rufai, Ukpon Akpan, ya roƙi kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa bisa haƙƙinsa na kundin tsarin mulki, domin ba shi damar shirya kariyarsa yadda ya kamata.

Sai dai, lauyoyin hukumar ICPC sun nuna rashin amincewarsu, inda suka bayyana cewa zarge-zargen da ake yi wa tsohon gwamnan suna da nauyi sosai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com