Tsohon Mataimakin Gwamna na Kwance, Wani Ya Rasu a Haɗarin da Ya Rutsa da Wakilan APC
- Taron shiyya na APC ya bar baya mara dadi sakamakon mummunan hadarin mota da ya rutsa da wasu daga cikin wakilan jam'iyya
- Rahotanni sun tabbatar da cewa wani mutum ya rasu,a hatsarin da ya rutsa da tsohon mataimakin gwamna a Katsina
- Lamarin ya rutsa da wakilan APC da ke kan hanyarsu zuwa taron yankin Arewa maso Yamma wanda aka yi a Kaduna
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna –Wakilan jam’iyyar APC daga ƙaramar hukumar Sabuwa a jihar Katsina sun gamu da mummunan hatsarin mota kafin su isa taron.
Wakilan sun hadu da bakar kaddara a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa taron jam’iyyar na yankin Arewa maso Yamma.

Source: Original
Daily Trust ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa hatsarin da ya faru ne kafin su isa wurin taron, ya haddasa asarar rai da kuma jikkatar wasu daga cikin mahalarta taron.
Wakilan jam'iyyar APC sun yi hadari
Rahoton ya bayyana cewa mutum guda daga cikin wakilan, mai suna Dalhat Machika, ya rasu sakamakon hatsarin.
Haka kuma, daga cikin waɗanda suka jikkata akwai tsohon mataimakin gwamnan jihar, Hon. Sirajo Umar Damari, da kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Sabuwa.
Wannan lamari ya jefa alhini da jimami a zukatan ‘yan jam’iyyar da al’ummar yankin, inda jama'a suka shiga cikin rudani.
Gwamnan Katsina ya ziyarci tawagar APC
A wata sanarwa da Mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Malam Ibrahim Kaula, ya fitar, ya bayyana cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti a jihar Kaduna domin samun kulawar likitoci.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce gwamna Malam Dikko Umaru Radda, bayan kammala taron yankin na APC, ya garzaya asibitin domin duba lafiyar waɗanda abin ya shafa.
A yayin ziyarar, gwamnan ya jajanta wa waɗanda suka jikkata da iyalansu, tare da yi masu addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa.
Gwamnan ya kuma tabbatar masu da cewa gwamnatin jihar Katsina za ta ci gaba da ba su cikakken goyon baya da kulawa a wannan lokaci mai wahala.
Gwamna Dikko Radda ya samu rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Hon. Ibrahim Kabir Masari.
Sai kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamna, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, tare da sauran manyan jami’ai.
Hadimin gwamna a APC ya yi murabus
A baya mun wallafa cewa jam'iyya mai mulki ta APC na ci gaba da rasa wasu 'ya'yanta yayin da ADC ke shirin tarkato kawunan 'yan adawa gabanin babban zaben 2027.
Daya daga cikin hadimin Uba Sani na Kaduna Hon. Yusuf Umar Garkuwa ya yi murabus daga mukaminsa na mai ba gwamna shawara tare da sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa.
Garkuwa ya fice daga jam’iyyar APC tare da mika shaidarsa na zama dan jam'iyya yayin da ya ke shirin hade wa da 'yan adawa a babbar jam'iyyar ta ADC mai tasowa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


