Trump Ya Aika wa Iran Bukatu 15 na Kawo Karshen Hare Haren Amurka da Isra'ila

Trump Ya Aika wa Iran Bukatu 15 na Kawo Karshen Hare Haren Amurka da Isra'ila

  • Donald Trump ya sanar da cewa Amurka tana tattaunawa da Iran yanzu haka kan wani tsarin zaman lafiya, kuma har an gabatar da bukatu 15
  • Daga cikin bukatun da Amurka ta gabatar, akwai tilasci ga Iran na daina tace sinadarin uranium tare da lalata dukkan kayyakin nukiliyarta
  • Amurka na duba yiwuwar tsagaita bude wuta na tsawon wata guda domin ba da damar tattaunawa kan wannan sabon tsarin sulhun

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - A ranar Talata, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa kasarsa tana tsaka da “tattaunawa” da kasar Iran, duk da cewa mahukuntan Tehran sun musanta batun yin tattaunawa kai-tsaye da Washington.

Trump, wanda ke magana daga ofishinsa na Oval Office, ya bayyana cewa ya janye barazanar da ya yi na kai hari kan matatun makamashin Iran ne saboda wannan tattaunawa da ya ce ake yi.

Kara karanta wannan

A karshe, Trump ya samu kasashe 3 da za su taimaka ya shawo kan Iran

Amurka ta gabatar wa Iran bukatu 15 na kawo karshen yakin su.
Shugaban Amurka, Donald Trump (hagu) da Ministan wajen Iran, Abbas Araghchi (dama) Hoto: Anna Moneymaker / ATTA KENARE via Getty Images
Source: Getty Images

Amurka ta gabatar da bukatun sulhu da Iran

Rahotanni daga jaridar The New York Times sun nuna cewa Amurka ta aika wa Iran wani daftarin sulhu mai bukatu 15 ta hannun kasar Pakistan.

Wannan tsari ya kunshi batutuwa masu sarkakiya da suka shafi shirye-shiryen makaman linzami na Iran, shirin nukiliya, da kuma tsaron mashigin ruwa na Hormuz.

Rahoton ya nuna cewa Amurka tana duba yiwuwar ayyana tsagaita bude wuta na tsawon wata guda domin ba da sararin gudanar da wadannan bukatu.

Wasu bukatun Amurka ga Iran

Wasu daga cikin sharudan da ke cikin daftarin sun hada da:

  • Lalata dukkan wasu makaman nukiliya da Iran take da su a halin yanzu.
  • Alkawarin cewa Iran za ta daina kokarin mallakar makamin nukiliya gaba daya.
  • Fitar da dukkan tataccen sinadarin uranium daga cikin kasar Iran zuwa waje.
  • Daina daukar nauyi ko bai wa kungiyoyin masu tsatstsauran ra'ayi dake yankin makamai.
  • Bude mashigar ruwan Hormuz ga kowa ba tare da tsangwama ba.

Kara karanta wannan

Pakistan za ta shiga tsakani a yakin Amurka da Isra'ila ke gwabzawa da Iran

Trump ya jaddada cewa hana Iran mallakar makamin nukiliya shi ne abu na “daya, biyu, da na uku” a cikin jerin abubuwan da Amurka ke bukata, in ji rahoton CNBC.

Donald Trump ya ce Amurka na kan tattauna wa da Iran don kawo karshen yakin su.
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi ga 'yan majalisar Republican a Doral, Florida. Hoto: Roberto Schmidt/Getty Images
Source: Getty Images

Ko Isra'ila za ta amince da kudurin Amurka?

Shugaba Trump ya bayyana sunayen manyan jami’an gwamnatinsa da ke da hannu a wannan tattaunawa, ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa JD Vance da Ministan Harkokin Waje Marco Rubio.

Haka kuma, an ambaci Steve Witkoff da Jared Kushner a matsayin wadanda suka tattauna da jami’an Iran a daren Lahadin da ya gabata.

Duk da wannan yunkuri, har yanzu ba a san matsayin kasar Isra'ila ba, wadda take kai wa Iran hari tare da Amurka, ko za ta amince da wannan tsarin na Trump.

Saudiya na so Amurka ta kai hari Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, Yarima Mohammed bin Salman ya bayyana yakin Iran a matsayin wata babbar dama ta sauya siyasar yankin Gabas ta Tsakiya.

Saudiyya ta karyata zargin ingiza Amurka zuwa yaki, inda ta ce babban burinta shine kare jama'arta daga hare-haren jiragen mara matuka.

Donald Trump ya ce ana tattaunawa mai kyau da Iran, amma mahukuntan Tehran sun karyata batun tattaunawar yayin da ake fafatawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com