An 'Bankado' Wani Aikin Sirri da Rasha ke Yi wa Kasar Iran a Yakinta da Isra'ila
- Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy ya yi magana kan yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka
- Zelenskiy ya ce kasarsa ta samu hujja karara cewa Rasha na bai wa Iran bayanan sirri, lamarin da zai kara tsawaita rikicin Gabas ta Tsakiya
- Shugaban ya ce Rasha na amfani da fasahar tattara bayanan sigina da hadin gwiwa da wasu kasashen yankin domin taimaka wa Iran wajen kai hare-hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kyiv, Ukraine - Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy ya yi tone-tone kan yakin da ake ci gaba da yi tsakanin Iran da Isra'ila.
Zelenskiy ya ce hukumomin leken asirin sojojin kasarsa sun samu hujja karara cewa Rasha na ci gaba da bai wa Iran bayanan sirri.

Source: Getty Images
Ya bayyana hakan ne bayan ganawa da shugaban leken asirin soja, inda ya ce wannan mataki na iya tsawaita rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya, cewar Reuters.
Martanin Rasha kan zargin taimaka wa Iran
Hakan ba shi ne karon farko ba da ake zargin Rasha na tallafa wa Iran da bayanan sirri domin samun galaba kan abokiyar gabanta, Isra'ila.
Sai dai hukumomi a Rasha sun sha mayar da martani kan zargin da cewa ko kadan ba su taimaka wa Iran a yakin da ake yi.
Kasar Rasha ta musanta rade-radin cewa tana taimaka wa Iran da bayanan sirri kan wuraren da kadarorin sojojin Amurka suke a yankin Gabas ta Tsakiya.
Kremlin ta sha musanta rahoton da ke cewa Rasha na bai wa Iran hotunan tauraron dan adam da ingantattun fasahohin jiragen yaki marasa matuki, tana kiran rahoton labarin karya.

Source: Getty Images
Zelenskiy: Zargin Rasha da agaza wa Iran
Zelenskiy ya kara da cewa Rasha na amfani da fasahar tattara bayanai da na yanar gizo, tare da bayanan da ta samu daga hadin gwiwa da wasu abokan hulda.
A cikin jawabin dare da ya saba gabatarwa, ya ce akwai karin hujjoji da ke nuna yadda Rasha ke kokarin aika bayanai ga Iran a boye.
Ya bayyana wannan aiki a matsayin mai illa sosai, yana mai cewa dole ne a dakatar da shi domin yana kara dagula al’amuran tsaro da zaman lafiya a duniya.
Zelenskiy ya kuma ce kasuwanni sun fara shiga damuwa, musamman a bangaren man fetur, yana mai gargadin cewa hakan na kara tsananta matsaloli a kasashe da dama, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Rasha ta fusata da harin Isra'ila a Lebanon
A wani labarin, Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta gayyaci jakadan Isra’ila Oded Joseph domin karin bayani kan harin da aka kai.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Isra'ila ta kai wani hari ya jikkata ‘yan jaridar RT a kasar Lebanon a yakin da ake yi wanda ya jawo asarar rayuka da dama.
Jakadan Isra’ila ya ki yin tsokaci ga manema labarai kafin ganawa a Moscow, yana mai cewa ba ya son makara yayin da ake jiran bayani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

