Baban Chinedu Ya Tona wa Fasto da Ya Kai Korafin Kisan Kiristoci Amurka Asiri
- Malam Yusuf Haruna wanda aka fi sani da Baban Chinedu ya dura kan Fasto Ezekiel Dachomo na jihar Plateau
- Baban Chinedu ya zargi Dachomo da kasancewa tsohon ɗan fashi, da ƙirƙirar labarin haduwarsa da Yesu bayan hari a banki
- Fasto Dachomo na daga cikin Fastoci da suka yi ta korafi kan zargin kisan Kiristoci da ya ja hankalin Amurka da Donald Trump
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Malam Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu, ya caccaki Fasto Ezekiel Dachomo.
Baban Chinedu ya zargi Fasto Dachomo daga Plateau da fashi da makami a shekarun baya a birnin Jos.

Source: Facebook
'Dachomo dan bindiga ne' - Baban Chinedu
Malam Yusuf Haruna ya fadi haka a shafin Facebook inda ya zarge shi da kasancewa tsohon ɗan fashi da makami, tare da cewa ya ƙirƙiri labarin haduwarsa da Yesu bayan wani harin banki a Jos.
Baban Chinedu ya bayyana cewa Dachomo ba wai kawai an gan shi da ‘yan bindiga ba ne, har ma shi kansa ɗan bindiga ne mai tarihin aikata laifi.
Ya ce akwai bayanai daga shekarar 1976 har zuwa bayan 2000 da ke nuna cewa Dachomo ya kasance gogaggen ɗan fashi mai hatsari.
A cikin bidiyon da ya bazu, ya kunna wani yanki inda Dachomo ya amsa cewa ya shiga fashin banki a shekarar 1980 a Jos tare da abokansa.
Sai dai Baban Chinedu ya musanta labarin, yana cewa ba gaskiya ba ne cewa mala’iku ko Yesu sun sauko domin ceton su a lokacin harin.
Ya ce a gaskiya bindigogi ne suka harbe su, kuma jami’an tsaro ne suka yi wannan aiki ba wani abin al’ajabi ba kamar yadda aka faɗa.
Shehin ya kara da cewa Dachomo ya ɓoya a cikin gawawwaki ne bayan an harbe su, sannan wani abokinsa mai suna Emmanuel ya taimaka masa ya tsira.
Ya kuma bayyana cewa wata mace ta shaida cewa Fasto Dachomo ya samu rauni daga harbin bindiga, kuma har yanzu yana da tabon raunin a jikinsa.

Kara karanta wannan
Yayin da Amurka ke ikirarin tattaunawa, Iran ta yi wa Isra'ila illa da makamai masu linzami

Source: Facebook
Zarge-zargen Baban Chinedu kan Dachomo
Baban Chinedu ya zargi Dachomo da sauyawa daga “ɗan fashi na zahiri” zuwa “ɗan fashi na sirri” wanda ke haddasa rikice-rikicen addini.
Ya ce irin wadannan mutane ne suka zama masu garkuwa da mutane a yau, suna haddasa tashin hankali a cikin al’umma.
Shehin ya kuma bukaci gwamnati da ta binciki Dachomo, yana mai cewa akwai yiwuwar yana da hannu a wasu ayyukan laifi
Haka kuma, ya kalubalanci Dachomo da ya kai shi kotu idan yana ganin akwai karya a cikin zarge-zargen da ake yi masa.
Sai dai wasu sun soki kalamansa, suna cewa ya yi hakan ne na kashin kai wanda zai iya kara rura wutar rikicin addini a Najeriya.
Fasto Dachomo ya caccaki Donald Trump
An ji cewa Fasto Ezekiel Dachomo a jihar Plateau ya nuna damuwa game da ƙaruwar hare-haren yan bindiga da ake yi a kwanakin nan.
Dachomo ya yi kira da a shirya shiga “yaki” da gaske inda ya zargi shugaban Amurka, Donald Trump da nuna wariya.
Ya ce ba za su kara gudu ba, suna shirye su mutu maimakon ci gaba da birne ‘yan uwansu bayan harin ramuwar gayya a Dorowa Babuje.
Asali: Legit.ng

