Abubakar Malami Ya ga Ta Kansa, EFCC Sun Shirya Kwance Masa Zani a Kasuwa

Abubakar Malami Ya ga Ta Kansa, EFCC Sun Shirya Kwance Masa Zani a Kasuwa

  • Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta kai samame gidan tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami a Maitama, Abuja
  • EFCC ta kai samame gidan ne domin kwace kadararsa ba tare da takardar kotu ba wanda ya jawo maganganu
  • Rahotanni sun nuna jami’an EFCC sun iso da motoci biyar, dauke da makamai, suka rufe hanyar shiga gidan, yayin da Malami ya amince su karbe gidan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jami’an hukumar yaki da cin hanci, EFCC sun kai samame gidan tsohon minista a Najeriya.

A yau Talata 24 ga watan Maris, 2026 jami'an suka kai samame gidan tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami da ke Maitama a Abuja domin kwace kadararsa.

EFCC sun mamaye gidan Abubakar Malami a Abuja
Jami'an hukumar EFCC a gidan Abubakar Malami a Abuja. Hoto: Abubakar Malami SAN, Abdulrahman Zakariyau.
Source: Facebook

Yadda EFCC suka mamaye gidan Abubakar Malami

An ruwaito cewa jami’an, karkashin jagorancin Folarin Sunday Dare, sun iso da kusan motoci biyar, sanye da rigunan aikinsu, dauke da makamai masu yawa, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Yayin da Amurka ke ikirarin tattaunawa, Iran ta yi wa Isra'ila illa da makamai masu linzami

Sun kuma rufe hanyar shiga gidan Malami, lamarin da ya hana mutane shiga ko fita, yayin da aka killace yankin baki daya domin gudanar da aikin.

Wani dan gidan Malami, Shehu Koko, ya tabbatar wa manema labarai cewa jami’an sun zo ba tare da nuna wata takardar kotu ba.

Ya ce Malami ya zabi fita cikin natsuwa domin kauce wa hayaniya da jami’an, inda ya basu damar karbar gidan ba tare da wata matsala ba.

Koko ya bayyana cewa:

“Sun ce sun zo ne da umarni daga sama domin kwace kadarar, kuma ba za ka iya yin fada da hukuma ba”.

Ya kara da cewa sun dauki lamarin a matsayin tsangwama ta siyasa, yana mai cewa Malami yana cikin koshin lafiya kuma yana da karfin zuciya sosai.

EFCC sun sake taso malami a gaba
Tsohon ministan Shari'a a Najeriya, Abubakar Malami. Hoto: Abubakar Malami.
Source: Facebook

EFCC sun shata gidan Abubakar Malami a Abuja

An kuma bayyana cewa a ranar Litinin jami’an sun fara yi wa gidajen alama, sannan a wannan rana suka zo domin kwace wannan gida na Maitama.

Kokarin shiga gidan da ke kusa da hanyar Amazon a Maitama ya ci tura saboda jami’an sun killace wurin gaba daya, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ce an kama 'malamin Musulunci' da ya karbe shi a Kaduna

A watan Janairun 2026, wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaka da haramtattun kudade.

Kotun ta kuma umarci EFCC da ta wallafa wannan umarni a jarida, tare da kiran masu ruwa da tsaki su bayyana dalilin da ya sa ba za a kwace kadarorin gaba daya ba.

A watan Fabrairun 2026, Malami ya kalubalanci wannan umarni ta hanyar gabatar da bukata a kotu yana mai adawa da kwace kadarorin da ake danganta masa.

Kotu ta umarci kama Abubakar Malami

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin tsare tsohon Antoni Janar Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a gidan gyaran hali na Kuje.

Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta aika da Malami tare da matarsa, Hajia Bashir Asabe, da dansu, Abubakar Abdulaziz Malami, zuwa gidajen yari.

Kotun ta ki amincewa da rokon belin da aka yi ta baki, inda ta bukaci lauyoyinsu su shigar da takarda a hukumance duba da nauyin zargin da ake musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.