Matakin Farko da Alkali Ya Dauka a Zaman Shari'ar El Rufai da Gwamnatin Najeriya
- Babbar Kotun Tarayya ta dage sauraron bukatar belin Nasir El-Rufai zuwa karshen watan Maris bayan ICPC ta gurfanar da shi kan zargin cin hanci
- An haramta wa manema labarai shiga cikin zauren kotun a Kaduna yau, yayin da jami'an tsaro suka mamaye ko'ina domin hana barkewar tarzoma
- Tsohon gwamnan yana fuskantar zarge-zargen almundahana da dukiyar kasa da kuma halatta kudaden haram a gaban kotuna daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a jihar Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar neman belin tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 31 ga watan Maris, 2026.
Wannan mataki ya biyo bayan zaman kotun na ranar Talata, inda lauyoyin ɓangarorin biyu suka gabatar da hujjojinsu a gaban alkali.

Source: Twitter
Kaduna: Kotu ta dage shari'ar El-Rufai
Lauyan El-Rufai, Ukpon Akpan, ya roƙi kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa bisa haƙƙinsa na kundin tsarin mulki, domin ba shi damar shirya kariyarsa yadda ya kamata, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan
Rana ba ta karya: Halin da ake ciki yayin da ICPC ta gurfanar da El Rufai a gaban kotu
Sai dai, lauyoyin hukumar ICPC sun nuna rashin amincewarsu, inda suka bayyana cewa zarge-zargen da ake yi wa tsohon gwamnan suna da nauyi sosai.
Lauyoyin sun kuma shaida wa kotun cewa bayar da belin El-Rufai, da irin wadannan tuhume-tuhume, na iya kawo cikas ga binciken da hukumar ke gudanarwa.
Bayan jin uzirin lauyoyin ICPC da na El-Rufai, kotun ta dage shari'ar zuwa ranar Talatar mako mai zuwa domin sauraron bukatar belin.
Sai dai, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Legit Hausa ba ta iya gano ko kotun ta ba da umarnin tsare El-Rufai a gidan yari, ko zai ci gaba da zama a hannun ICPC ba.
Zarge-zargen da ICPC ke yi wa El-Rufai
Hukumar yaƙi da cin hanci da hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (ICPC) ce ta gurfanar da El-Rufai tare da wani mutum mai suna Joel Adoga, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.
Ana zarginsu da laifuffuka da suka haɗa da karkatar da dukiyar gwamnati, mallakar kadarorin jama'a ba bisa ƙa'ida ba, da kuma halatta kuɗaɗen haram a ƙarƙashin ƙara mai lamba FHC/KD/73/2026.

Kara karanta wannan
Uwargidan tsohon gwamnan Kaduna, Hadiza Nasir El Rufai ta rasu? An ji gaskiyar batu
Mun ruwaito cewa, baya ga wannan ƙara a Babbar Kotun Tarayya, ICPC ta kuma shigar da wata daban a Kotun Shari'a ta jihar Kaduna mai lamba KDH/KAD/ICPC/01/26.
A can ma ana zargin tsohon gwamnan da Amadu Sule da laifin cin zarafin ofis, zamba, da kuma amfani da iko wajen neman alfanu ga kai. Dukkan waɗannan ƙararraki an shigar da su ne tun ranar 18 ga Maris, 2026.

Source: Twitter
An hana 'yan jarida shiga kotu
A lokacin da aka gurfanar da El-Rufai a ranar Talata, an tsaurara matakan tsaro sosai a cikin birnin Kaduna da kuma kewayen harabar kotun, in ji rahoton Punch.
Jami'an tsaro dauke da makamai sun mamaye manyan hanyoyin shiga kotun domin dakile duk wani tarzoma da ka iya tasowa daga magoya bayan tsohon gwamnan da suka taru a waje.
Wani abin lura shi ne yadda aka hana 'yan jarida shiga cikin zauren kotun domin shaida yadda shari'ar ke gudana, kamar yadda muka ruwaito.
Yayin da aka sanya ranar 31 ga Maris 2026 don ci gaba da shari'ar a kotun tarayya, har yanzu ba a ayyana ranar da za a fara sauraron wadda take kotun jihar ba.

Kara karanta wannan
ICPC ta sanya lokacin gurfanar da El Rufai gaban kotu bayan kwashe dogon lokaci a tsare
El-Rufai ya yi karar hukumar DSS
A wani labari, mun ruwaito cewa, Nasir El-Rufai ya nemi kotu ta soke tuhumar da hukumar DSS ke masa tare da biyan sa diyyar Naira biliyan biyu.
Lauyoyin tsohon gwamnan na Kaduna sun gabatar da hujjoji guda 17 inda suka ce tuhumar ta saba wa hakkin dan adam da kundin tsarin mulki.
Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ce za ta saurari wannan bukata a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2026 a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng