Rana ba Ta Karya: Halin da Ake ciki yayin da ICPC Ta Gurfanar da El Rufai gaban Kotu
- Nasir El-Rufai ya isa birnin Kaduna bayan ya kwashe kwanaki yana tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC
- Tsohon gwamnan na Kaduna zai gurfana ne a gaban babbar kotun tarayya kan tuhume-tuhumen da hukumar ICPC ke yi masa
- Malam Nasir El-Rufai ya isa harabar kotun bayan samun rakiyar dumbin jami'an tsaro yayin da ake shirin fara sauraron shari'ar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya isa babbar kotun tarayya da ke Kaduna a safiyar ranar Talata, 24 ga watan Maris 2026.
El-Rufai ya isa kotun ne cikin tsauraran matakan tsaro domin gurfanar da shi kan zargin laifuffukan da suka shafi cin hanci da rashawa.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce an kawo El-Rufai harabar kotun da misalin ƙarfe 9:00 na safe a cikin wata motar Hilux.
ICPC ta gurfanar da Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan ya zauna a ciki na tsawon fiye da mintuna 30 kafin a raka shi cikin babban zauren kotun da misalin ƙarfe 9:34 na safe, jaridar Leadership ta dauko rahoton.
Sanye da babbar riga koriya mai haske da hula mai launi ɗaya, an tsaurara tsaro a kansa yayin da jami'an hukumar ICPC da na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suka kewaye shi har zuwa cikin zauren kotun.
An jibge jami'an tsaro a kotun
Sai dai kuma, jami'an DSS sun hana ’yan jarida damar shiga cikin zauren kotun, waɗanda suka isa wurin tun da sanyin safiya da misalin ƙarfe 7:00 na safe don ɗaukar rahoton yadda shari'ar ke gudana.
Tuni aka tsaurara matakan tsaro a kewayen harabar kotun da ke tsohuwar makarantar horar da sojoji ta NDA, inda aka baza jami'an tsaro dauke da makamai tun da sanyin safiyar ranar.
Tawagar tsaron ta ƙunshi jami'an DSS, rundunar 'yan sandan Najeriya, ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL), da kuma jami'an tsaro na hukumar NSCDC.

Kara karanta wannan
ICPC ta sanya lokacin gurfanar da El Rufai gaban kotu bayan kwashe dogon lokaci a tsare

Source: Twitter
An takaita zirga-zirgar ababen hawa
An taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a yankin, lamarin da ya tilasta wa masu ababen hawa bin hannu ɗaya daga hanyar Unguwar Sarki zuwa Kawo, wanda hakan ya janyo cunkoson ababen hawa.
Wannan ci gaba ya biyo bayan sanarwar da hukumar ICPC ta fitar a baya cewa za ta gurfanar da El-Rufai a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna a yau Talata, 24 ga Maris, 2026.
Kotu ta amince da bukatar ICPC kan El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta amince da bukatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gabatar a shari'arta da Malam Nasir El-Rufai.
Kotun ta ba hukumar ICPC izinin bincika tare da nazarin na'urorin da aka kwashe daga gidan tsohon gwamnan na jihar Kaduna.
Mai shari'a Joyce Abdulmalik wadda ke jagorantar shari'ar ta ba da umarnin ne biyo bayan wata buƙata ta gaggawa da hukumar ICPC ta shigar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
