Shirin Gwamna Na Komawa APC Ya Jawo an Fara Gudun Gwamnatinsa
- Gwamnan jihar Zamfara ya rasa daya cikin kwamishinonin da ke aiki a gwamnatinsa sakamakon murabus din da wani daga cikinsu ya yi
- Kwamishinan ilmi, kimiyya da fasaha, Mallam Wadatau Madawaki, ya yanke shawarar yin murabus daga mukaminsa
- Wadatau Madawaki ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda a ganinsa yin hakan shi ne abin da ya fi dacewa ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Gusau, jihar Zamfara - Daya daga cikin kwamishinoni a gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ya yi murabus.
Kwamishinan ilmi, kimiyya da fasaha na jihar Zamfara, Mallam Wadatau Madawaki, ya yi murabus daga mukaminsa.

Source: Facebook
Mallam Madawaki ya tabbatar da hakan ga tashar Channels Tv ta hanyar tattaunawa a wayar tarho.
Meyasa kwamishinan ya yi murabus?
Kwamishinan ya bayyana shirin ficewar Gwamna Dauda Lawal zuwa jam’iyyar APC a matsayin dalilin ɗaukar matakin nasa.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Dangote ya gano matsalolin da yakin Amurka, Iran zai jefa 'yan Najeriya
Ya bayyana cewa ya kasance jajirtaccen ɗan jam’iyyar PDP kuma ba shi da niyyar shiga jam’iyyar APC.
“Na yi murabus ne kawai saboda Gwamnan zai koma APC, ni ɗan PDP ne, ban taɓa zama ɗan APC ba kuma ban shirya na zama ɗan APC ba.”
- Mallam Wadatau Madawaki
Shin Gwamna Dauda ya tilasta masa?
Yayin da yake amsa tambayoyi kan ko an matsa masa lamba ne ya yi murabus, tsohon kwamishinan ya musanta kowane nau'in takura, inda ya nuna cewa a karan kansa ya yanke shawarar yin hakan.
“Gwamna bai taɓa tilasta wa kowa ya yi murabus ba, har ma a lokacin taron masu ruwa da tsaki, ya faɗa cewa babu wanda za a tursasa wa ya shiga jam’iyyar, na yi murabus ne kawai saboda ina ganin hakan shi ne abin mutunci da ya kamata na yi.”
- Mallam Wadatau Madawaki

Source: Facebook
Gwamna Dauda ya amince da murabus dinsa
A halin da ake ciki, Gwamna Dauda Lawal ya amince da murabus ɗin kwamishinan, jaridar Premium Times ta kawo labarin.
Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya bayyana cewa an umarci Kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Abdulmalik Abubakar Gajam, da ya kula da ma’aikatar ilimi a matsayin mai riƙon ƙwarya nan take.
Gwamna Lawal ya nuna kwarin gwiwa kan kwarewar Gajam wajen tabbatar da ci gaba da daidaito a fannin ilimi na jihar.
Haka kuma gwamnan ya gode wa tsohon kwamishinan kan hidimar da ya yi, sannan ya yi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.
Shettima zai karbi Gwamna Dauda zuwa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shirye-shirye sun kankama na tarbar gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, zuwa jam'iyyar APC bayan ya sauya sheka daga PDP mai adawa a Najeriya.
Ana sa ran Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ne zai jagoranci karbar Gwamna Dauda Lawal zuwa cikin jam’iyyar a ranar Talata, 24 ga watan Maris, 2026.
Shugaban APC na jihar Zamfara, Tukur Danfulani Maikatako ya nuna farin cikin jam’iyyar bisa dawowar Gwamna Lawal APC, yana mai cewa mataimakin Shugaban Kasa tare da shugabannin jam’iyyar na kasa za su halarci bikin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
