Yan Ta'adda da Jami'an Tsaro Sun Fafata ana Shirin Kama Jagoran Ƴan Bindiga a Kano
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta dakile hari yayin yunƙurin cafke wani da ake zargi shugaban ‘yan bindiga ne a Kano
- Rikici ya ɓarke bayan wanda ake zargi ya tsere, ya shiga taron jama'a tare da tunzura mutane suka far wa yan sanda
- Yanzu haka jami'an sun dauki sabon mataki domin a samu nasarar kamo wadanda suka tsere yayin da ake zurfafa bincike
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce ta dakile wani hari da aka kai wa jami’anta da ke kokarin kama jagoran yan ta'adda.
Rundunar ta ce jami'an sun kai wani samame domin cafke wani da ake zargi shugaban ‘yan bindiga ne a Karamar Hukumar Bichi.

Source: Original
Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da 6.30 na yammacin ranar 22 ga watan Maris, 2026.
'Yan sanda sun yi aiki a Kano
Rahoton ya bayyana cewa jami'an yan sanda sun kai 'dauki bayan samun kiran gaggawa daga ofishin ‘yan sanda na Tudun Wulli. A cewar majiyoyin, wata tawaga ta rundunar yaki da masu garkuwa da mutane, karkashin jagorancin ASP Abubakar Musa, ta bi sahihan bayanan sirri kan wasuyan ta'adda.

Source: Facebook
Bayanan sun tabbatar da cewa an gano wani da ake zargi shugaban ‘yan bindiga ne mai suna Muhammad, wanda aka fi sani da “Senator” ko “Kirchi” a Bichi.
Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin ya je kauyen Tudun Wulli ne domin halartar bukukuwan Sallah, lamarin da ya ba jami’an tsaro damar gano inda yake.
Abin da yan sanda suka gano
Majiyar ta ce an hango wanda ake zargin dauke da bindigar AK-47, amma da jami’an ‘yan sanda suka yi yunƙurin cafke shi, sai ya tsere cikin wani taron jama’a.
“Nan take al’amura suka rikice yayin da wasu daga cikin jama’ar suka fara jifar jami’an ‘yan sanda da duwatsu da wasu makamai masu hadari."
A sakamakon haka, an jikkata ASP Lawali Hamidu, sannan aka lalata gilashin motar sintiri ta rundunar.
Jami'an sun yi gaggawar janyewa da dabarun tsaro, mutane hudu sun samu raunukan harbi, inda aka garzaya da su zuwa Asibitin Gwamnati na Bichi domin samun kulawa.
Daga cikin wadanda suka jikkata, wata mata mai suna Halima Saidu ta rasu daga baya, kamar yadda likita ya tabbatar, yayin da sauran ke samun sauki a karkashin kulawar likitoci.
An samu nasarar kwashe dukkannin jami’an tsaron da suka shiga aikin cikin koshin lafiya, yayin da aka kara tura karin jami’an tsaro zuwa yankin domin hana sake barkewar tashin hankali. Rundunar ‘yan sandan ta ce an shawo kan lamarin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin da kuma cafke wanda ake zargi da ya tsere.
'Yan ta'adda sun kai hari Kano
A baya, kun samu labarin cewa wasu ƴan ta'adda aƙalla shida sun sace sakataren mulki na Karamar Hukumar Kibiya, Hon. Hamza Musa Durba har gida.
Maharan sun kutsa kauyen a kan babura dauke da bindigu a daren Asabar 20 ga watan Maris, 2026 inda suka shiga gidan jami'in gwamnatin da makamansu.
Rahotanni sun bayyana cewa sun sace jami'in duk da an sanar da jami'an tsaro, amma sun kammala aikin da ya kai su kauyen a cikin sauri kafin a kawo dauki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

