Da Gaske 'Yan Bindiga 150 Sun Nutse cikin Kogi a Sokoto? An Ji Gaskiyar Zance
- An yada wasu rahotanni masu ikirarin cewa 'yan bindiga 150 sun nutse a cikin kogi a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma
- Rahotannin sun yi ikirarin cewa 'yan bindigan sun nutse ne bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya gamu da hatsari
- Mazaunan yankin, rundunar 'yan sanda da hukumar NIWA sun yi magana kan gaskiyar lamarin da ake ta yayatawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Hukumar kula da sufurin ruwa ta kasa (NIWA) ta yi martani kan rahotannin da ke cewa 'yan bindiga 150 sun nutse cikin kogi a Sokoto.
Hukunar NIWA ta ƙaryata rahotannin da ke iƙirarin cewa kimanin ’yan bindiga 150 sun nutse a hatsarin jirgin ruwa a yankin Sabon Gida na ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce shugaban NIWA mai kula da ofishin shiyyar Sokoto, Bello Bala, ya yi watsi da rahoton a matsayin ƙarya a ranar Litinin, 23 ga watan Maris 2026 a Sokoto.
An musanta nutsewar 'yan bindiga a Sokoto
Bello Bala ya ce babu wani lamari makamancin haka da ya faru, inda ya ƙara da cewa kogin da aka ambata ba hanyar ruwa ce da jirage ke iya bi ba.
Ya yi kira ga kafofin yaɗa labarai da su kiyaye wajen yaɗa labaran ƙarya, sannan su riƙa tantance labarai daga majiyoyi masu inganci, tare da tabbatar da cewa hukumar a shirye take ta bayar da ƙarin bayani a kowane lokaci.
A gefe guda, wata majiya daga runduna ta 8 ta sojojin ƙasa ta Najeriya da ke Sokoto ita ma ta tabbatar da cewa rahoton ƙarya ne, tana mai bayyana cewa babu wani lamari makamancin haka da ya faru a yankin.
Me Mutanen yankin suka ce?
Mazauna garin Sabon Gida da ke ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto sun yi watsi da batun nutsewar 'yan bindigan a cikin kogi.
Wasu mazauna yankin da suka tattauna da jaridar Daily Trust sun musanta faruwar lamarin a yankin, inda suka nuna cewa babu wani babban kogi da zai iya haddasa hatsarin da za a iya nutsewa.
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ita ma ta ƙaryata rahoton.
Kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya bayyana iƙirarin a matsayin “tsabagen ƙarya,” inda ya jaddada cewa ba a rubuta faruwar irin wannan lamari a ko'ina a jihar ba.
“Wuri ɗaya ne kawai muke da shi da aka sani da Sabon Gida, wani ƙauye ne a ƙaramar hukumar Gada. Bincikenmu ya tabbatar da cewa babu wani babban kogi a wurin, balle har a samu yanayin da fasinjoji za su iya nutsewa."
“DPO mai kula da yankin shi ma ya tabbatar da cewa babu wani lamari makamancin haka da ya faru a ƙaramar hukumar Gada."
- DSP Ahmad Rufai

Source: Original
'Yan bindiga sun farmaki cocin Kwara
A wani labarin kuma, kuma kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a wata coci da ke jihar Kwara ana tsaka da gudanar da ibada.
'Yan bindigan sun farmaki cocin ECWA da ke yankin Omugo, a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, inda suka yi awon gaba da wasu masu ibada.
Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun afka cikin harabar cocin ne tare da sace mutane da dama kafin jami’an tsaro su kawo dauki.
Asali: Legit.ng

