Gwamnatin Kano Ta Fadi Abin da Ya Hana Abba Tarbar Sarki Sanusi a Hawan Nasarawa
- Gwamnatin Kano ta karyata zargin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi fatali da Sarki Muhammadu Sanusi II
- Rahotanni sun yawaita a kan yadda aka gudanar da Hawan Nasarawa ba tare da an ga fuskar Gwamna Abba Kabir Yusuf ba
- Wannan na jawo martanin gwamnati, inda ta wanke duk wani zargi da ake yi na cewa akwai baraka a tsakanin Abba da masarauta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta yi martani kan wani rahoton da ke zargin cewa Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya yi watsi da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Rahoton hakan ya biyo bayan rashin ganin Gwamna ya tarbi Sarki Sanusi II yayin gudanar da Hawan Nasarawa a Fadar Gwamnatin Kano.

Source: Facebook
Sai dai Darakta janar kan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature D-Tofa ya warware dalilan da suka jawo hakan ta faru a sakon da ya wallafa a Facebook.
Gwamnatin Kano ta magantu kan hawan Nasarawa
A cikin sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin 23 ga watan Maris, 2026, gwamnatin ta bayyana rahoton akwai sabani tsakanin Gwamna da masarauta a matsayin mara tushe.
Sanarwar ta ce zargin ba gaskiya ba ne ko kadan, kuma an kirkiro shi ne domin yaudarar jama’a da kuma haifar da rudani a cikin al’umma.
Gwamnatin ta jaddada cewa babu wani abu makamancin haka da ya faru, kuma akwai alaka mai kyau tsakanin gwamnatin Kano da masarauta.
Ta kara da cewa irin wadannan rahotanni na karya na iya haddasa rashin fahimta da kuma barazana ga zaman lafiya, don haka ya kamata jama’a su rika tantance labarai.
Abin da ya hana gwamna zuwa Hawan Nasarawa
Gwamnatin ta bayyana cewa a al’adance, gwamnoni kan halarci wasu muhimman taruka na kasa musamman a lokacin bukukuwan Sallah.

Source: Facebook
A bana, bikin Hawan Nasarawa ya zo daidai da wani muhimmin taron gwamnonin Najeriya, wanda hakan ya tilasta wa Gwamna Abba Yusuf fita daga jihar domin halartar taron.
Kafin tafiyarsa, gwamnan ya sanar da Sarkin Kano halin da ake ciki, sannan ya umarci kakakin majalisar dokokin jihar da wasu manyan jami’an gwamnati su karbi bakuncin Sarkin a madadinsa a Fadar Gwamnati.
Haka kuma, gwamnatin ta tunatar da cewa gwamnan ya halarci sallar Idi da Sarkin Kano ya jagoranta, sannan ya halarci Hawan Daushe a masarautar Gaya.
Sanarwar ta kara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma halarci shirye-shiryen karbar sarakunan Rano da Karaye da Gaya da kansa.
Sai dai saboda aiki da ya taso ba zato ba tsammani, an wakilta wasu manyan jami’ai su tsaya masa a wasu daga cikin wadannan bukukuwa.
A lokacin da ake gudanar da Hawan Nasarawa, gwamnan yana birnin Legas ne domin halartar wani taro na hukuma tare da sauran gwamnoni.

Kara karanta wannan
Bayan fiye da shekara 1, gwamnatin Kano ta waiwayi iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi
Gwamnatin Kano ta jaddada cewa babu wata matsala ko sabani tsakaninta da Majalisar Masarautar Kano, inda ta ce dangantakar da ke tsakaninsu tana nan daram bisa mutunta juna.
Aminu Ado ya aika sako ga Gwamnatin Kano
A baya, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gudanar da sallar Idi a birnin Kano a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris 2026.
Aminu Ado Bayero ya aika da sako ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kano kan su ci gaba da kokari wajen sauke nauyin da ke kansu na taimakon jama'a.
Mai martaba sarkin ya aika da sako na musamman ga Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bayan kammala azumin watan Ramadan duk da bai yi hawa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

