Faransa za Ta Bi Sahun Amurka, Za a kawo wa Najeriya Agaji a kan Rashin Tsaro

Faransa za Ta Bi Sahun Amurka, Za a kawo wa Najeriya Agaji a kan Rashin Tsaro

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rashin tsaro a matsayin babbar barazana ga ci gaban Najeriya
  • Shugaban ya bayyana cewa a haɗin gwiwa da ƙasashen waje da jihohi zai taimaka wajen murƙushe ta’addanci
  • Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bayan Amurka, akwai wasu kasashen da ke shirin tallafa wa don yaki da ta'addanci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana rashin tsaro a matsayin babban ƙalubale na gaba da gwamnatinsa za ta fuskanta.

A cewarsa, hakan yana zama barazana kai tsaye ga ci gaba da bunƙasar tattalin arzikin Najeriya, wanda ba haka aka so ba.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce za a samu dauki
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a yayin wani taro a kasar waje Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

TVC News ta wallafa cewa Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin kungiyar gwamnoni a gidansa da ke Legas, inda ya ke hutun karamar Sallah.

Kara karanta wannan

"Yan ta'adda na amfani da bidiyon azabtarwa don firgita al’umma": Masani ya bayar da mafita

Najeriya ta sabunta da kasashen waje

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Tinubu ya bayyana haka ne bayan dawowarsa daga ziyarar aiki mai muhimmanci da ya kai Birtaniya.

Shugaban ya jaddada cewa sabunta haɗin gwiwa da ƙasashen duniya tare da ƙarfafa alaƙa da gwamnatocin jihohi zai zama muhimmin mataki wajen kawo ƙarshen ta’addanci.

Bayan kammala tattaunawa da manyan shugabanni a Birtaniya, Tinubu ya ce ya nuna aniyarsa ta fuskantar matsalar rashin tsaro kai ka-in-da-na-in.

Faransa za ta taimaka wa Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Emmanuel Macron Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Ya kuma yaba wa gwamnonin jihohi bisa goyon bayan da suka ba shi yayin ziyarar, yana mai cewa halartar su alama ce ta haɗin kai da amincewa da gwamnatinsa.

Faransa za ta taimaki Najeriya

Tinubu ya bayyana cewa tattaunawar da aka yi a Birtaniya da kuma gwamnatin Faransa sun fi karkata ne kan samar da kayan aiki da tallafin ayyuka ga hukumomin tsaron Najeriya.

Haka kuma, ya yi gargadin cewa rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya na iya janyo matsin tattalin arziki, wanda zai iya haifar da tashin farashi da rage ƙarfin aljihun jama'a.

Kara karanta wannan

Trump ya soki NATO, ya yi magana game da ƙasashen da suka ki taya su yaƙar Iran

Ya amince cewa wannan na iya ƙara matsin lamba daga ƙungiyoyin ƙwadago wajen neman inganta walwalar ma’aikata, amma ya bukaci gwamnonin jihohi su fifita bukatun talakawa

Shugaban ya kuma mika ta'aziyya da jaje ga Mataimakinsa Kashim Shettima wanda ya wakilce shi wajen kai sakon gwamnati bayan harin da aka kai Maiduguri.

Yakin Iran ya taba Najeriya

A baya, kun samu labarin cewa litar man fetur ta kusa kai ₦1,400 a sassan Najeriya sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya saboda rikicin Amurka, Isra'ila da Iran.

Direbobin motocin kasuwa a Legas da Kano sun koka kan yadda yanzu ba sa samun riba, yayin da matafiya ke fama da tsadar kudin sufuri a kasar nan bayan fara yakin.

Wasu da aka zanta da su, sun bayyana irin radadin da suke ji game da wannan karin kudin, wanda ake fargabar zai ci gaba da tashi a nan gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng