Trump Ya Juyo kan Najeriya, Amurka Ta Sake Turo Daruruwan Sojoji, Jiragen Yaƙi Ƙasar

Trump Ya Juyo kan Najeriya, Amurka Ta Sake Turo Daruruwan Sojoji, Jiragen Yaƙi Ƙasar

  • Kasar Amurka ta sake tura jiragen MQ-9 da sojoji 200 zuwa Najeriya domin ci gaba da tallafawa a yaki da ta'addanci a kasar
  • Hukumomin Najeriya sun ce sojojin Amurka na aiki daga filin jirgin Bauchi, suna taimakawa gano da bibiyar barazanar ‘yan ta’adda a Arewa
  • Matakin ya biyo bayan karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP, yayin da hadin gwiwar kasashen biyu ke kara karfi wajen yaki da ta’addanci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kasar Amurka ta tura jiragen sama marasa matuki na MQ-9 tare da kusan sojoji 200 zuwa Najeriya domin bayar da taimakon leken asiri da horaswa.

Aikin yana mayar da hankali ne kan tattara bayanai da ba da shawara, ba tare da sojojin Amurka sun shiga gaba wajen yaki ko kai hare-hare ba.

Kara karanta wannan

Trump zai sauya salon yaki da Iran, sojojin Amurka 2,500 sun nufi Gabas ta Tsakiya

Amurka ta sake turo sojoji Najeriya
Shugaba Donald Trump na Amurka da Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Jami’an Amurka da Najeriya sun shaida cewa an tura jiragen MQ-9 domin taimaka wa sojoji wajen gano da bibiyar barazanar ‘yan ta’adda, cewar Punch.

Yadda hukumomin Najeriya suka nemi taimakon Amurka

Rahotanni sun nuna cewa hukumomin Najeriya ne suka nemi wannan taimako domin inganta yaki da kungiyoyin ta’addanci a yankunan Arewa.

Wani jami’in tsaron Amurka ya bayyana cewa suna kallon barazanar tsaro a matsayin matsala ta bai daya, tare da jaddada cewa aikin na leken asiri ne kawai.

Manjo Janar Samaila Uba ya tabbatar da cewa sojojin Amurka na aiki daga filin jirgin sama na Bauchi a yankin Arewa maso Gabas.

Ya ce wannan hadin gwiwa na kara inganta sabuwar cibiyar hadin bayanan sirri tsakanin Amurka da Najeriya, domin tallafawa kwamandojin filin daga.

Jiragen MQ-9 na iya shawagi sama na tsawon lokaci, suna tattara bayanai kuma suna da damar kai hari, amma a yanzu ana amfani da su ne kawai don sa ido.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe Boko Haram kusan 100 suna shirin kai hari ana gobe sallah

Jami’an sun ce sojojin Amurka na taimakawa Najeriya wajen gano da bibiyar barazanar ‘yan ta’adda ba tare da bayyana cikakken bayani kan ayyuka ba.

Amurka na ci gaba da taimakawa Najeriya a yaki da ta'addanci
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yana addu'a a masallaci. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Musabbabin zuwan sojojin Amurka Najeria

Wannan mataki ya zo ne yayin da hare-haren ta’addanci ke karuwa a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na Najeriya.

Sojojin Najeriya sun ce tsawon lokacin zaman sojojin Amurka zai dogara ne da yarjejeniya tsakanin kasashen biyu a wannan hadin gwiwa.

Hakan na nuna karin mayar da hankali kan musayar bayanan sirri da karfafa kwarewar sojoji wajen fuskantar sababbin barazanar tsaro a Najeriya.

Rahoton ya kuma biyo bayan hare-haren sama da Amurka ta kai a ranar Kirsimeti bisa umarnin Donald Trump kan ‘yan ta’adda masu alaka da ISIS, cewar Business Insider Africa.

Jami’an Amurka sun ce wannan mataki na da nufin kara karfafa kokarin Najeriya wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda a fadin kasar.

Amurka za ta sayar da makamai ga Larabawa

An ji cewa kasar Amurka ta amince da yarjejeniyar sayar da makamai na dala biliyan 16.5 ga kasashe makwabtan Iran.

Kara karanta wannan

Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa

Hakan ya biyo bayan ci gaba da yaki da ake yi tsakanin Iran da kasar Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Kasashen da Amurka ta kulla yarjejeniyar da su sun hada Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait da Jordan yayin da rikici da Iran ke kara tsananta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.