"Yan Ta'adda na Amfani da Bidiyon Azabtarwa don Firgita Al’umma": Masani Ya Bayar da Mafita
A cikin ƴan kwanakin nan, ƴan ta'adda sun ƙara ƙarfafa miyagun ayyukansu ta hanyar baje su a kafofin sada zumunta.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Marigayi Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa, wani ɗalibin NYSC a yankin Sokoto da Zamfara, da wasu mata biyu – na daga cikin mutanen da aka ga ƴan ta'adda na wulakanta su tare da nuna su a shafukan sada zumunta.

Source: Twitter
Wani Hausawa ya wallafa wani bidiyo a shafin Facebook da ke nuna ƴan ta’adda suna murnar karɓar kuɗin fansa da ya haura Naira miliyan 50.
Wannan na daga cikin bidiyoyi da dama da ake yadawa a Facebook, TikTok da sauran kafafen sada zumunta na cin zarafi, azabtar da bayin Allah ko karɓan kuɗin fansa
An hango matsala da salon ƴan ta’adda
Dr. Sulaiman Ishaq Muhammad na tsangayar ilimin halayyar ɗan adam da laifuffuka ta jami’ar tarayya Dutse, jihar Jigawa, ya shaida wa Legit cewa akwai babbar matsala a yadda ƴan ta’adda ke amfani da kafafen sada zumunta.
A kalamansa:
"Abin da zai sa mai laifi ya kawo abin da ya aikata kan kafofin sadarwa har ya yi bajakoli da shi, yana nuna akwai rauni a tsarin tsaro, kuma akwai gibi a yadda Najeriya ke karɓar kafofin sadarwa daga ƙasashen waje."
"Kowace ƙasa idan za a shigar mata da irin waɗannan kafofi, musamman TikTok, Facebook da Twitter (X), sai an tsara dokoki da ƙa’idojin da za su kayyade abubuwan da za a iya wallafawa."

Source: Twitter
Dr. Sulaiman Ishaq Muhammad ya ƙara da cewa sakacin da ake yi wajen sarrafa kafafen sada zumunta na jawo barazana iri-iri da suka haɗa da:
1. Barazana ga ɗa’ar ɗan adam
2. Barazana ga tsaron ƙasa
3.Nuna raunin gwamnati kan dokokin kafafen sada zumunta
4. Bai wa masu garkuwa da mutane damar baje kolin ayyukansu
5. Barazana ga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su
6. Koyar da matasa aikata laifin garkuwa da mutane
7. Samar da hanyar sadarwa kai tsaye tsakanin ƴan ta’adda da matasa masu sha’awar aikata laifi
Shawarar masani kan matsalar ƴan ta’adda
Dr. Sulaiman Ishaq Muhammad ya ce yadda aka ga ƴan ta’adda sun wulakanta Sarkin Gobir da wani ɗalibin hidimar ƙasa ya isa ya sa Najeriya ta farka domin dakile wata babbar barazana.
Ya ce:
"Tun da sun fara amfani da kafofin sadarwa, wannan yana nuna suna amfani da hankalin jama’a. Idan ka lura, wuraren da suke zuwa su wallafa irin waɗannan bidiyoyi ba lallai su ne inda suke tsare mutanen ba. Bayan sun gama, sukan mayar da su wuraren ɓoyewa da ba a sani ba."
Ya bayar da wasu shawarwari da suka hada da:
1. Ƙarfafa bibiya ta intanet
Dr. Sulaiman Ishaq Muhammad ya ce akwai gibi a yadda gwamnati ke bibiyar muhimman abubuwa a kafafen sada zumunta.
A kalamansa:
"Ya kamata gwamnati ta zuba jari wajen bunƙasa ilimin 'cyber forensics', wanda zai ba da damar gano yadda aka wallafa abu, inda aka wallafa shi, da kuma motsin sa bayan an fitar da shi."
Ya ce ƙarfafa wannan fanni zai taimaka wajen gano hanyoyin da ƴan ta’adda ke bi bayan sun wallafa bidiyon cin zarafin ɗan adam.
2. Dakile bayar da kuɗin fansa
Ya bayyana cewa ƙasashe kamar Ingila da Amurka sun daɗe suna yaƙi da biyan kuɗin fansa saboda illarsa.
A cewarsa:
"Matukar ana biyan kuɗin fansa, ana ƙarfafa su, ana ba su damar sayen makamai da ci gaba da aikata laifuka."
Sai dai ya ce yawaitar yaɗa bidiyon cin zarafi na tilasta iyalai biyan kuɗin fansa domin ceto ƴan uwansu.
3. Horas da jami’an tsaro
Ya ƙara da cewa akwai buƙatar a horas da jami’an tsaro kamar DSS, NSA da ‘yan sanda kan amfani da fasahohin zamani.

Source: Facebook
Ya ce dole ne a samar musu da ingantattun kayan aiki da dabarun 'access control' domin bibiyar ayyukan ƴan ta’adda a intanet.
Ya zargi Najeriya da sakaci wajen ɗaukar matakan da ƙasashe irin su Isra’ila da Amurka ke ɗauka wajen sa ido kan abubuwan da ake wallafawa, ciki har da haramta fitar da bidiyo ko hotunan da ke ƙarfafa ta’addanci.
Dr. Ishaq Muhammad Sukai ya ce akwai buƙatar a farka tun yanzu, kafin matsalar ta yi girman da za ta zama babbar kalubale ga tsaron kasa.
Ƴan ta'adda sun kai hari Kano
A baya, kun samu labarin cewa wasu ƴan ta'adda aƙalla shida sun sace sakataren mulki na Karamar Hukumar Kibiya, Hon. Hamza Musa Durba.
Maharan sun kutsa kauyen a kan babura dauke da bindigu a daren Asabar 20 ga watan Maris, 2026 da suka shiga gidan jami'in gwamnatin da manyan makamai.
Rahotanni sun sace duk da an sanar da jami'an tsaro, ƴan ta'addan sun yi gaggawar kammala abin da ya kai su, sannan suka yi awon gaba da jami'in.o
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



