Manya: Najeriya za Ta Warware Matsalar da Yakin Iran da Amurka Ta Haifar
- Ministan yada labarai na kasa, Mohammed Idris, ya ce Najeriya a shirye take ta taimaka wajen magance rikicin makamashi da ke faruwa a duniya
- Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi a rikicin Gabas ta Tsakiya, a wata hira da ya yi
- Kalaman Mohammed Idris sun fara janyo martani iri-iri daga ‘yan Najeriya, inda wasu suka koka cewa har yanzu kasar ba ta iya biyan bukatun cikin gida ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Britain - Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na taimakawa wajen magance matsalar makamashi a duniya ta hanyar samar da danyen mai ga kasashen da ke bukata.
Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris ne ya bayyana haka bayan rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi sakamakon yakin da Amurka da Isra’ila suka fara.

Source: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa Mohammed Idris ya sanar da hakan ne a wata hira da ya yi da BBC ta wallafa a shafinta na X yayin zuwan shugaba Bola Tinubu Birtaniya.
Gudunmawar Najeriya a yakin Iran/Amurka
Rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi ya haifar da matsalar makamashi a duniya, lamarin da ya janyo tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, sai dai ministan ya ce Najeriya a shirye take ta cike gibin da ke kasuwar mai.
Da yake magana, ya ce:
“Mu ‘yan Najeriya muna son hada kai da sauran kasashen duniya. Najeriya a shirye take ko yaushe ta bayar da gudunmawa wajen tabbatar da tsaron makamashi a duniya.
"Duk abin da Najeriya za ta iya yi domin rage tashin hankali, za ta yi. Duniya na bukatar mai, kuma Najeriya tana nan. Za mu ci gaba da tabbatar da cewa duniya na samun karin man Najeriya idan ya zama dole.”
Martanin 'yan Najeriya kan batun
Legit ta rahoto cewa kalaman ministan yada labaran sun janyo ra’ayoyi mabambanta daga ‘yan Najeriya, musamman masu amfani da kafar X.
Arinze Maduekwe ya bayyana dalilin da ya sa Najeriya ba za ta iya magance matsalar mai ta duniya ba:
“Me ya sa ku ke bata lokaci da kafafen yada labarai kuna fadin abubuwan da kuka san ba gaskiya ba? Najeriya ma ba ta iya cika adadin da OPEC ta dora mata tsawon shekaru ba. Har lamarin ya kai ga OPEC ta bai wa wasu kasashe rabon Najeriya.”
Nimsy Robert ya ce har yanzu Najeriya ba ta cika bukatun kanta ba:
“‘A shirye take ta samar da mai…’ Wannan kamar wasa ne! Ba za ka iya bayar da abin da ka wuce bukatarka ba alhali ba ka iya cika naka.
"A yanzu ana samar da ganga miliyan 1.3 a rana, kasa da adadin 1.5 na OPEC, alhali kasafin 2026 ya tanadi ganga miliyan 1.84 a rana. Don Allah ku farka daga mafarkin da kuke.”
Tunde ya bukaci ‘yan Najeriya su kasance masu kishin kasa:
“Ku daina fadin maganganu marasa kyau kan Najeriya; da yawa daga cikinku ba ku taba fita kasashen waje ba, shi ya sa ba ku ganin darajar abin da kuke da shi.”

Source: Twitter
Ga bidiyon hirar BBC da Mohammed Idris:
Amurka ta cirewa Iran takunkumi
A wani labarin, kun ji cewa matsin lambar tattalin arziki ta sanya gwamnatin Amurka cirewa Iran takunkumin sayar da mai ga kasashen duniya.
Gwamnatin Trump ta dauki matakin ne a daidai lokacin da farashin mai da gas ke kara tashi a Amurka da fadin duniya saboda yakin da ake.
Iran ta toshe mashigar Hormuz da wasu kasashen duniya ke bi domin jigilar danyen mai ta teku, lamarin da ya jawo koma baya a kasuwar makamashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


