A Wani Yanayi na Daban, Sanusi II Ya Jagoranci Sallar Idi a Kano, Aminu Ado Ya Ware a Fadarsa
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Idi a Kofar Mata, inda ya fito a kafa saboda dokar hana hawan doki
- Ya bukaci jama’a su ci gaba da hakuri da taimako, tare da gargadin matasa su guji tashin hankali su mayar da hankali ga ilimi da sana’o’i
- A gefe guda, Aminu Ado Bayero ya gudanar da salla a fadarsa ta Nasarawa, yayin da tsaro ya yi karfi amma an gudanar da bukukuwan lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Idi a filin Idi na Kofar Mata domin kammala watan Ramadan cikin kwanciyar hankali.
A wani sauyi na daban, Sarkin ya fito daga fadar Gidan Rumfa a kafa domin gudanar da Hawan Idi, sakamakon dokar gwamnati ta hana hawan doki.

Source: Twitter
Abba da manya sun halarci idin Sarki Sanusi II
Sanusi II ya isa ta hanyoyin da aka tsara tare da jagorantar dubban masu ibada, inda gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran manyan jami’an gwamnati suka halarta, cewar Daily Trust.
Sai dai mataimakin gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo bai halarta ba, inda aka ce yana gudanar da sallah tare da Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa.
Bayan sallah, Sarkin ya yi jawabi a Kofar Kwaru inda ya gode wa Allah bisa kammala Ramadan lafiya cikin kwanciyar hankali.
Ya bukaci jama’a su ci gaba da hakuri da taimako da ladabi, tare da kira ga hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Sarkin ya gargadi matasa su guji tashin hankali, yana karfafa musu gwiwa su nemi ilimi da koyon sana’o’i masu amfani a rayuwarsu.
Gargadin Sanusi II ga yan kasuwa
Har ila yau, ya gargadi ‘yan kasuwa su guji karin farashi ba bisa ka’ida ba, tare da yi wa wadanda suka yi asara a gobara addu’a.

Kara karanta wannan
'Ku yi koyi da Annabi SAW': Malami ga Sanusi II, Aminu Bayero kan hawan salla a Kano
Sarkin ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan ayyukan raya kasa da yaki da daba, yana mai kira ga jama’a su mara masa baya.
Ya kammala da addu’ar samun zaman lafiya a Kano da Arewacin Najeriya, da kuma ga wadanda fashewar Borno ta shafa, cewar rahoton Punch.

Source: Twitter
Aminu Ado ya ja hankalin al'ummar Kano
A gefe guda, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya gudanar da sallar Idi a fadarsa ta Nasarawa tare da dimbin jama’a.
Taron ya samu halartar masu sarauta da malamai da mazauna gari, inda aka gudanar da sallar cikin tsari da nutsuwa.
A jawabinsa, Bayero ya gode wa Allah bisa kammala Ramadan, tare da kira ga jama’a su zauna lafiya su kuma bi doka.
Duk da tsauraran matakan tsaro a Kano, an gudanar da bukukuwan idi cikin kwanciyar hankali da walwala a tsakanin jama’a.
Idi: Malami ya ja hankalin Sanusi II, Bayero
A baya, an ji cewa wani malamin addini a Kano ya roƙi Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II su guji rikici kan shirin gudanar da hawan Sallah.
Ya yi gargadin cewa dagewa kan gudanar da hawa biyu a lokaci guda na iya haddasa rikici, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya ga cigaba.
Malamin ya buƙaci gwamnati da jami’an tsaro su dauki matakan kariya, yana mai cewa duk shugaba za a yi masa hisabi a ranar lahira kan ayyukansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

