Yadda Gwamnati Ta Yi Ganawar Sirri da Sarki gabanin Sanar da Hawan Sallah a Kano

Yadda Gwamnati Ta Yi Ganawar Sirri da Sarki gabanin Sanar da Hawan Sallah a Kano

  • Tawagar gwamnan Kano ta yi ganawar sirri da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a bayan an yi buda baki
  • Wannan na zuwa ne yayin da rikicin kujerar sarauta tsakanin Sarki Sanusi II da Alhaji Aminu Ado Bayero ke ci gaba da ɗaukar hankali
  • An yi wannan tattaunawa ne gabanin sanar da cewa Khalifa Muhammadu Sanusi II zai jagoranci hawan Sallah a bana

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aike da wata tawaga ta musamman da ta gana da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II gabanin sanar da shirin hawan Sallah a jihar.

Manyan sun saka labule a wani taro na sirri da aka gudanar a fadar Gidan Rumfa, lamarin da ya ƙara jawo hankali kan rikicin sarautar da ke gudana a jihar.

Kara karanta wannan

'Ku yi koyi da Annabi SAW': Malami ga Sanusi II, Aminu Bayero kan hawan salla a Kano

Gwamnatin Kano ta aika tawaga ga Sarki Sanusi II
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II tare da tawagar gwamnatin jiha Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hadimin Gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa ne ya sanar da zantawar a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 19 ga watan Maris, 2026.

Tawagar gwamnati ta gana da Sarkin Kano

Daily Trust ta wallafa cewa ganawar ta zo ne sa’o’i kaɗan bayan Sarkin ya karɓi manyan jami’an gwamnati a wajen buda baki da ya shirya a fadarsa, wanda ya haɗa shugabanni da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da al’umma.

Sanusi Bature ya bayyana cewa tawagar gwamnan ta ƙunshi Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Umar Ibrahim, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Sulaiman Wali Sani, tare da shi kansa.

An gana da Sarkin Kano jim kadan bayan buda baki a yammacin Talata
Sanusi Bature D-Tofa tare da Sarki Muhammadu Sanusi II Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A cewarsa:

“Jim kadan bayan an kammala Iftar a fadar Sarki, tawagar gwamna ta yi ganawar sirri da Mai Martaba.”

Wannan ganawa ta zo a daidai lokacin da jihar Kano ke shirin bukukuwan karamar Sallah, musamman hawan Durbar wanda ya shahara a tarihi da al’adun Hausawa tsawon ƙarni.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

Ana fuskantar kalubale game da hawan Sallah

A shekarar 2024 ne gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da Sanusi II kan karagar mulki, amma Sarki Aminu Ado Bayero bai amince da matakin ba, inda ya garzaya kotu domin kalubalantar tsige shi.

Tun daga lokacin, batun sarautar Kano ya ci gaba da janyo muhawara a fagen siyasa da shari’a, tare da sanya al’ummar jihar cikin jiran yadda al’amura za su kaya.

Ko da yake gwamnatin jihar ta nuna alamun cewa rikicin na iya samun mafita nan ba da jimawa ba, ganawar buda bakin da kuma tattaunawar sirri da ta biyo baya sun nuna alamun ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnati da Sanusi II.

Masu sharhi na ganin cewa halartar tawagar gwamna a wadannan taruka biyu na nuni da yadda gwamnati ke kallon Sanusi II a matsayin halastaccen Sarkin Kano duk da rikicin da ke gudana.

Sarki Muhammadu Sanusi II zai yi hawan Sallah

A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin Kano ta dakatar da Hawan Daushe da sauran hawan dawakai saboda rahotannin sirri dake nuna shirin wasu mutane na tayar da tarzoma.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tura sako ga Shugaban ƙasa game da harin bama bamai a Maiduguri

Sarki Muhammad Sanusi II ne zai jagoranci Hawan Idi, yayin da aka soke Hawan Fanisau da Dorayi domin tabbatar da tsaron jama'a da dukiyoyinsu a faɗin jihar.

Jami'an tsaro sun samu umarnin tsananta sanya ido da kuma daukar mataki kan duk wanda ya nemi tada hankali a lokacin bukukuwan Sallah karama da ke tafe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng