Sanusi II ko Aminu Ado?: An Fadi 'Sarkin' da Zai Jagoranci Hawan Sallah a Kano
- Gwamnatin Kano ta dakatar da Hawan Daushe da sauran hawan dawakai saboda rahotannin sirri dake nuna shirin wasu mutane na tayar da tarzoma
- Sarki Muhammad Sanusi II ne zai jagoranci Hawan Idi, yayin da aka soke Hawan Fanisau da Dorayi domin tabbatar da tsaron jama'a da dukiyoyinsu
- Jami'an tsaro sun samu umarnin tsananta sanya ido da kuma daukar mataki kan duk wanda ya nemi tada hankali a lokacin bukukuwan Sallar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta sanar da sauye-sauye masu muhimmanci ga bukukuwan al'adu na wannan ƙaramar Sallar.
Wannan mataki ya biyo bayan rahotannin sirri da gwamnatin ta samu daga Kwamitin Tsaro na Jiha, waɗanda ke nuna cewa wasu bata-gari na shirin haddasa tarzoma a lokacin bukukuwan Sallar.

Source: Facebook
Sallah: An gano shirin tada tarzoma a Kano
Mai tallafawa gwamnan Kano, Ibrahim Adam ne ya ya fitar da sanarwar hakan a shafinsa na Facebook, wacce ya ce ta fito ne daga kwamishinan yada labarai da al'adu, Comrd. Ibrahim Abdullahi Waiya.
Gwamnatin ta jaddada cewa ko da yake tana matukar da kiyaye wa da bunkasa al'adun Kano, amma ta ce babban nauyin da ya rataya a wuyanta shi ne kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Sanarwar kwamishinan ta ce:
"Gwamnatin Kano na son sanar da al'umma cewa ta samu sahihan rahotannin sirri daga majalisar tsaro ta jiha, inda aka gano wasu bata-gari na shirin tayar da tarzoma da karya doka da oda yayin bukukuwan karamar Sallah mai zuwa.
"Gwamnatin na jaddada cewa ba za ta kauce daga babban nauyin da ya rataya a wuyanta ba, na tabbatar da zaman lafiya, bin doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar."

Kara karanta wannan
Musulmai na shirin karamar Sallah, dakarun NSCDC sun mamaye muhimman wurare a Kano
An sauya tsarin bukukuwan Sallah a Kano
Bayan tattaunawa da Masarautar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta amince da tsarin bukukuwan Sallah kamar haka:
1. Hawan Idi:
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ne zai jagoranci wannan hawa daga filin sallar Idi na Kofar Mata ta hanyoyin da aka ayyana zuwa Gidan Shettima, inda za a kammala a Kofar Fatalwa ta fadar Sarkin Kano.
2. Hawan Nasarawa:
Za a gudanar da wannan hawa a wani salo na daban, amma ba za a yi shi a kan dawakai ba.
3. Hawan Daushe:
Gwamnati ta dakatar da wannan hawa a halin yanzu, inda ta bayyana cewa za a ci gaba da yin sa a bukukuwan Sallah na gaba in-sha-Allah.
4. Hawan Fanisau da Hawan Dorayi:
Waɗannan hawa guda biyu ma an dakatar da su a yanzu domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron jama'a.

Source: Facebook
Gwamnati ta gargadi al'ummar Kano
Gwamnatin ta bayyar da umarni ga dukkan jami'an tsaro da su tsananta sanya ido da tabbatar da an bi waɗannan dokoki sau da ƙafa, cewar rahoton Daily Trust.
Haka zalika, an umarci jami'an da su ɗauki dukkan matakan shari'a domin hana duk wani yunkuri na tayar da hankali kafin Sallah, lokacin Sallah, da kuma bayan shagulgulan.
A ƙarshe, gwamnatin ta yi kira ga dukkan mazauna jihar da su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka, kuma su ba jami'an tsaro haɗin kai.
Ta kuma gargaɗi mutane da su guji yaɗa labaran ƙarya waɗanda ba a tantance ba, tana mai yi wa dukkan al'ummar Musulmi fatan alheri da murnar zagayowar wannan babban biki na ƙaramar Sallah.
Sanusi II ba zai yi hawan Sallah ba?
Tun da fari, kun dai ji cewa, gwamnatin Kano ta yi karin haske game da wata sanarwa da ke nuna cewa wai ta ce ba Sarki Muhammadu Sanusi II ne zai jagoranci hawan sallah a 2026 ba.
Kwamishinan yada labaran Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya ya karyata takardar da ke yawo cewa gwamnati ta ce ba Sanusi II ne zai jagoranci hawan sallar ba.
Ibrahim Waiya ya ce ko kadan wannan sanarwa ba daga ofishinsa ta fita ba, kuma ba a fitar da ita a madadin gwamnatin jihar Kano ba, don haka ya nemi a yi watsi da ita.
Asali: Legit.ng

