El Rufa'i Ya Fara Samun Nasara a kan Gwamnati bayan Kotu Ta Soke Wani Hukunci
- Kotun daukaka kara ta soke hukuncin kotun tarayya kan shari’ar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai
- Daga cikin dalilan da kotun tallata bayar na soke hukuncin, ta ce ce an take masa hakkinsa na sauraron shari’a yadda ya kamata
- An mayar da shari’ar domin a sake sauraro a gaban wani alkalin daban yayin da El-Rufa'i ke hannun ICPC kan wasu zarge-zargen
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna –Kotun daukaka kara da ke zamanta a Kaduna ta soke hukuncin da kotun tarayya ta yanke a wata kara da tsohon gwamna, Nasir El-Rufai, ya shigar a kan majalisar dokokin jihar.
A hukuncin da kotun ta yanke kan ƙorafin daukaka kara mai lamba CA/K/240/2024, kotun ta bayyana cewa an samu kura-kurai a shari’ar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yuli, 2024.

Kara karanta wannan
Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa

Source: Twitter
The Sun ta wallafa cewa kotun ta ce ba a mika wa Nasir El-Rufai takardar sanarwar kotu yadda ya kamata ba, kuma hakan ya hana shi damar mayar da martani ga takardun da wadanda ake kara suka gabatar.
Kotu ta soke hukuncin kotun tarayya kan El-Rufa'i
New Telegraph ta ruwaito cewa kotun daukaka karar ta bayyana cewa hukuncin da alkalin kotun tarayya, Mai shari’a R.M. Aikawa, ya yanke a ranar 30 ga watan Yuli, 2024, bai inganta ba.
Saboda haka, kotun ta ayyana hukuncin a matsayin maras tushe tare da umartar a mayar da shari’ar zuwa kotun tarayya domin a sake ba wa wani alkalin daban.
Kotun ta jaddada cewa isar da takardun sanarwar shari’a yadda ya kamata na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da hurumin kotu.
Ta kuma ce hana Nasir El-Rufai damar kare kansa ya sabawa ka’idojin shari’a da ke karkashin dokar kare hakkin dan Adam.
Yadda El-Rufa'i ya shigar da kara
Tun da farko, El-Rufai ya shigar da karar ne a shekarar 2024 domin neman a kare masa hakkinsa na dan Adam.
Ya zargi Majalisar dokokin jihar Kaduna da hana shi cikakken damar kare kansa yayin binciken da ta gudanar a kansa.

Source: Facebook
Wannan hukunci na kotun daukaka kara ya zama babban nasara ga tsohon gwamnan, domin ya ba shi damar sake gabatar da karar tasa a gaban kotu.
Hakan na nufin za a sake duba dukkanin bayanan shari’ar daga tushe a karkashin sabon alkalin da za a nada don sauraron ƙarar.
El-Rufa'i ya samu matsala a kotu
A wani labarin, kun ji cewa kotu ta sahalewa hukumar ICPC ta ci gaba da tsare tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a binciken da ta ke masa.
Hukumar CPC na zargin El-Rufa'i da almundahana yayin da ta garkame shi na sama da kwanaki 20 bayan ya fito daga ofishin EFCC da ya kai kansa.
Tuni lauyansa ya garzaya kotu yana neman a soke sabon umarnin da hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati ta samu, inda ya ke ganin an saɓa ka'ida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

