Kotu Ta Umarci Musulmi Sharar Masallaci bayan Sata yayin Rabon Abincin Azumi
- Abin al'ajabi bai karewa, an cafke wani mutum a Abuja bayan satar waya a masallaci yayin da ake cikin azumin watan Ramadan
- Wata kotu a Abuja ta yanke wa wani mutum hukuncin share masallaci na wata guda kan satar wayar lantarki
- An kama Musa Ibrahim da laifin satar wayar mai darajar N2m a cikin masallaci lokacin da ake rabon abincin azumi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata kotun majistare da ke Abuja ta yanke hukunci kan wani dan kasuwa game da satar wayar lantarki a cikin masallaci.
Wanda ake tuhumar Musa Ibrahim tuni ya amsa laifinsa na satar lantarki a masallaci a cikin watan azumin Ramadan mai alfarma.

Source: Original
kotun ta umurce shi da ya rika share harabar masallacin Annur da ke wuse ii na tsawon wata guda a matsayin hukunci, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan
Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa
An kama barawon Alkur'ani a masallacin Abuja
A daidai wannan wata a shekarar 2024 ma, wata kotu ta daure wani mutum a Abuja kan abin kunya da ya yi na satar Alkur'ani mai girma a masallaci.
Kotun ta ɗaure lebura tsawon watanni 15 a gidan gyaran hali bayan kama shi da laifin satar Alƙur'ani a wani Masallaci da ke Abuja.
Alkalin kotun mai zama a Abuja, mai shari'a Malam Aliyu Kagarko, ya bai wa mutumin mai suna, Terkaa Akishi, zaɓin tarar N40,000.
Tun farko mai gabatar da kara daga hukumar ƴan sanda ya ce sun kwato kayayyakin da mutumin ya sace yayin gudanar da bincike.

Source: Twitter
Yadda mutumin ya lallaba cikin masallaci
Mai gabatar da kara, A. A. Adeleju, ya bayyana wa kotu cewa wanda ake tuhuma ya shiga masallacin ne a ranar 5 ga Maris, 2026 lokacin rabon abincin Ramadan.
Ya ce yayin da mutane ke tsaye a layi domin karbar abinci, sai wanda ake tuhuma ya bi ta kofar baya ya cire wayar lantarki na masallacin.
A cewar mai gabatar da karar, binciken ‘yan sanda ya nuna cewa Musa Ibrahim ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
An kuma gano cewa wayar da ya sata na da darajar kusan Naira miliyan biyu, kuma an kwato shi daga hannunsa.
A lokacin shari’a, wanda ake tuhuma ya roki kotu da ta sassauta masa, yana mai alkawarin cewa ba zai sake aikata irin wannan laifi ba.
Daga bisani, alkalin kotun Lami Sani ta yanke masa hukunci bayan ya amsa laifukan barna da sata.
An kama dattijo da sata a masallacin Kaduna
A baya, mun ba ku labarin cewa jama'a sun yi ram da wani ɗattijo ɗan shekara 74 wanda ke sace masu tabarman masallacin unguwa a Rigasa, ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna.
Mutumin mai suna Jibril Musa ya amsa laifinsa, inda ya ce ya jima yana ƴan ɗauke-ɗauke a masallatai amma bai taɓa satar Alƙur'ani ba.
Jibril da ake zargi da laifin satar, ya bayyana hanyar da yake bi wajen satar, ya ce yana sayar da duk tabarma ɗaya a kan N1,500 zuwa N2,000.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
