Harin Bam a Borno: Sanata Ndume Ya Faɗawa Tinubu abin da Ya Kamata Ya Yi

Harin Bam a Borno: Sanata Ndume Ya Faɗawa Tinubu abin da Ya Kamata Ya Yi

  • Sanata Ali Ndume ya fadawa Shugaba Bola Tinubu cewa tsaron rayukan 'yan Najeriya ya fi siyasar 2027 muhimmanci
  • Ndume ya nemi Tinubu ya ziyarci Borno ko ya tura mataimakinsa domin jajanta wa iyalan mutane 25 da bam ya kashe
  • Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yi magana game da wadanda harin bama-bamai ya kashe a Maiduguri

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Sanata Ali Ndume, ya yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta ba da fifiko ga batun tsaron ‘yan ƙasa maimakon maida hankali kan shirye-shiryen siyasar 2027.

Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja.

Sanata Ali Ndume ya bukaci Tinubu ya mayar da hankali kan tsaro maimakon siyasar 2027
Sanata Ali Ndume ya na gabatar da jawabi a zauren majalisar dattawa. Hoto: Muhammed Ali Ndume
Source: Facebook

Sakon Sanata Ali Ndume ga Tinubu

Ali Ndume ya nuna damuwarsa kan yadda rayukan mutane ke salwanta a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu ya fadi abin da mahaifinsa ke yi wa Najeriya da ba a sani ba

Sanatan ya jaddada cewa "masu fita su kaɗa ƙuri'a na mutuwa kullum," don haka ya bukaci shugaban ƙasa da ya dauki mataki, a gani a ƙasa, ba wai ya tsaya a maganganu kawai ba.

Ya bayyana cewa har yanzu akwai mutane da dama da ba a gan su ba tun bayan kisan kiyashin da aka yi a Ngoshe, wannan ya ce abin takaici ne matuka.

Sannan Sanata Ndume ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbata ta kamo waɗanda suka kai hare-haren bama-bamai na ranar Litinin a Maiduguri don hukunta su.

Shawarwarin Ndume ga gwamnatin tarayya

Sanata Ali Ndume ya ba da shawarar cewa idan Shugaba Tinubu ba zai iya ziyartar jihar Borno ba, to ya tura mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, domin ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnati na damuwa da halin da suke ciki.

Ya kuma bukaci a daina nuna halin ko-o-ho ga matsanancin rashin tsaro da ƙasa ke ciki, inda ya ce babban nauyin kowace gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Shettima ya magantu kan harin Borno

Kashim Shettima ya nuna takaicinsa kan mutuwar mutane 25 a hare haren bam a Borno
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a fadar shugaban kasa, Abuja. Hoto: @officialSKSM
Source: Twitter

A gefe guda kuma, Kashim Shettima ya bayyana alhininsa kan rasuwar mutane 25 da suka rasa rayukansu a hare-haren bama-baman na Maiduguri.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin da ya sa 'yan ta'adda suka tayar da bam a Maiduguri

Shettima ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata yayin rufe karatun Tafsirin Ramadan na shekara-shekara a masallacin fadar shugaban ƙasa dake Abuja, in ji rahoton Punch.

Mataimakin shugaban ya jaddada cewa babu wani addini da ya amince da kashe rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, inda ya yi addu'ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu.

Tinubu ya yi magana kan harin Borno

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da hare-haren 'yan kunar bakin wake da aka kai Maiduguri.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa 'yan ta'addan suna kai hare-haren ne saboda yadda jami'an tsaro suka matsa musu lamba a dazuka.

Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da daukar matakan da suka dace domin magance barazanar 'yan ta'adda a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com