Musulmai na Shirin Karamar Sallah, Dakarun NSCDC Sun Mamaye Muhimman Wurare a Kano
- An jibge dakarun rundunar NSCDC fiye da 3,400 a sassa daban-daban na jihar Kano domin tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan karamar Sallah
- Kwamandan NSCDC na jihar Kano, Mohammed Hassan-Agalama ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da rundunar ta fitar yau Talata a Kano
- Hassan-Agalama ya bayyana cewa an jibge jami’an tsaron a wurare masu muhimmanci domin tsare al'umma da dukiyoyinsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Rundunar tsaron al'umma (NSCDC) reshen jihar Kano ta fara shirye-shirye da daukar matakan tabbatar da tsari a lokacin shagulgulan karamar Sallah mai zuwa..
Rundunar NSCDC ta sanar da tura jami’ai sama da 3,400 sassa daban-daban na jihar Kano domin tabbatar da tsaro kafin, yayin da kuma bayan bukukuwan Eid al-Fitr.

Source: Twitter
Dalilin tura jami’an tsaro Kano
Vanguard ta rahoto cewa kwamandan NSCDC a jihar, Mohammed Hassan-Agalama, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a, Ibrahim Idris-Abdullahi, ya fitar a ranar Talata a Kano.
A cewarsa, wannan mataki na daga cikin shirin kariya da rundunar ta dauka tun kafin lokaci domin kare muhimman kadarorin kasa tare da tabbatar da cewa an gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali.
Wuraren da aka tura dakarun NSCDC a Kano
Hassan-Agalama ya bayyana cewa an jibge jami’an tsaron a wurare masu muhimmanci da suka hada da filayen sallar Idi, wuraren shakatawa, kasuwanni, tashoshin mota dasauran wuraren taruwar jama’a.
Ya kara da cewa rundunar za ta ba da kulawa ta musamman ga muhimman ababen more rayuwa, kamar tashoshin lantarki, wuraren samar da ruwa da kuma hasumiyoyin sadarwa.
Kwamandan ya kuma ce rundunar tsaron ta kara karfafa bangaren leken asiri da sa ido, sannan kuma ta tanadi jami'ai na musamman don daukar matakin gaggawa idan bukatar hakan ta taso.
NSCDC ta aika sako ga al’umma
Hassan-Agalama ya bukaci mazauna jihar Kano da su kasance masu sanya ido da lura, su hada kai da jami’an tsaro, su kuma kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga jami’an tsaro mafi kusa.

Kara karanta wannan
Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi
Haka kuma ya shawarci iyaye da masu kula da yara da su gargadi ‘ya’yansu su guji aikata duk wani abu da zai iya tayar da hankali ko karya doka.

Source: Original
A karshe, ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa rundunar NSCDC ta kuduri aniyar kare rayuka da dukiyoyi, tare da kira ga jama’a su gudanar da bukukuwan Sallah cikin natsuwa da zaman lafiya.
Yaushe za a yi karamar Sallah?
A dazu, mun kawo muku cewa Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci a fara duban jinjirin watan Shawwal daga gobe Laraba, 29 ga Ramadan, 1447AH.
Sultan ya bukaci al’ummar Musulmi a fadin Nigeria da su nemi jinjirin watan Shawwal wanda zai nuna karshen watan azumin Ramadan da kuma ranar hawa idin Karamar Sallah.
Ganin jinjirin watan Shawwal, 1447 shi ke nuna cewa watan azumin Ramadan na bana ya kare, daga nan za a fara bukukuwan Sallah Karama (Eid El-Fitr).
Asali: Legit.ng
