Azumi Ya Zo Karshe, Sarkin Musulmi Ya Fitar Sanarwa kan Ranar Karamar Sallah a Najeriya

Azumi Ya Zo Karshe, Sarkin Musulmi Ya Fitar Sanarwa kan Ranar Karamar Sallah a Najeriya

  • Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci a fara duban jinjirin watan Shawwal daga gobe Laraba, 29 ga Ramadan, 1447AH
  • Ya bukaci duk wanda ya ga watan ya sanar da Hakimi ko Mai Unguwa mafi kusa da shi domin isar da sakon ga fadar Sarkin Musulmi
  • Idan aka ga watan a gobe Laraba, hakan na nufin za a yi karamar Sallah ranar Alhamis, amma idan ba a gani ba, sallah za ta kama ranar Juma'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NCIA), Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya nemi a fara duban watan Karamar Sallah.

Sultan ya bukaci al’ummar Musulmi a fadin Nigeria da su fara neman jinjirin watan Shawwal wanda zai nuna karshen watan azumin Ramadan da kuma ranar hawa idin Karamar Sallah.

Kara karanta wannan

Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri

Mai Alfarma Sarkin Musulmi.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III a fadarsa da ke Sakkwato Hoto: Dailar Usmaniyya
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da fadar Sarkin Musulmin ta wallafa a shafinta na Facebook, yau Talata, 28 ga watan Ramadan, 1447AH daidai da 17 ga watan Maris, 2026.

Ranar fara duban watan Sallah a Najeriya

Sanarwar wacce Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa za a fara duban watan ne ranar Laraba.

Sanarwar ta ce:

“Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, na kira ga Musulmi a fadin kasar nan da su nemi jinjirin watan Shawwal a ranar Laraba, 18 ga Maris, 2026."

Yadda mutum zai kai sakon ganin wata

Ta kara da cewa duk Musulmin da ya ga jinjirin watan ya kai rahoton ganin sa ga Hakimi ko Mai Unguwa mafi kusa da shi, domin isar da sakon ga Majalisar Sarkin Musulmi don tabbatarwa.

Kara karanta wannan

Ana batun azumi 30, Saudiyya ta fitar da sanarwa game da ranar karamar Sallah

“Musulman da suka ga sabon watan su sanar da ga Hakimi ko Mai Unguwa mafi kusa, wanda shi kuma zai isar da wannan bayani ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, domin yin sanarwa ta gaba,” in ji sanarwar.
Wata.
Yadda ake hango jinjirin watan Musulunci a sararin samaniya Hoto: @theharamain
Source: Twitter

Lambobin da za a kira idan an ga wata

Fadar Sarkin Musulmi ta kuma bayar da wasu lambobin waya na musamman domin kai rahoton ganin jinjirin wata kai tsaye ga ofishin kwamitin ganin Mal.

Lambobin sun su ne: 0803 715 7100, 0806 630 3077, 0803 596 5322, 0803 594 5903, 0706 714 6900

Ganin jinjirin watan Shawwal, 1447 yana nufin karshen watan azumin Ramadan, da kuma fara bukukuwan Sallah Karama (Eid El-Fitr).

Za a fara duban watan Shawwal a Saudiyya

A wani labarin, kun ji cewa Saudiyya ta bukaci musulmi su fara duban jinjirin watan Shawwal daga yammacin ranar Laraba, 29 ga watan Ramadan, 1447AH.

A sanarwar da Saudiyya ta fitar, ta ce sakamakon duba jinjirin watan da za yi a ranar Laraba mai zuwa ne zai tabbatar da ranar idin karamar Sallah (Eid al‑Fitr).

Hukumomim Saudiyya sun kuma yi kira ga duk wanda ya ga jinjirin watan da idonsa ko ta hanyar na’ura, da ya garzaya kotu mafi kusa domin bada shaida.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262