Tinubu Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Ta'adda Suka Tayar da Bam a Maiduguri

Tinubu Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Ta'adda Suka Tayar da Bam a Maiduguri

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da hare-haren 'yan kunar bakin wake da aka kai birnin Maiduguri na jihar Borno
  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa hare-haren sun shafi wurare uku kuma sun jawo mutuwar jama'a da dama da jikkata wasu
  • Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da daukar matakan da suka dace domin magance barazanar 'yan ta'adda a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya magantu bayan harin da ake zargi 'yan Boko Haram ne suka kai Maiduguri da dare.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban kasar ya yi magana ne jim kadan bayan tashin jirginsa zuwa Birtaniya a wata ziyara da ya shirya kaiwa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fara neman sauran ƴan ƙunar baƙin wake a Borno, an nemi daukin jama'a

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu da hafsoshin tsaro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Maganar Tinubu kan harin Maiduguri

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Bola Tinubu ya ce abubuwan da suka faru a Maiduguri sun tayar da hankalin al'umma matuka.

Ya ce:

"Labaran da suka fito daga Maiduguri, jihar Borno, sun matukar tayar da hankali. Ina alhinin wadanda suka rasa rayukansu, na tausaya wa wadanda suka jikkata, kuma ina tare da al’ummar Borno a wannan lokaci na damuwa."

Me yasa aka kai hari Maiduguri?

Shugaba ya kara da cewa 'yan ta'addan suna kai hare-haren ne saboda yadda jami'an tsaro suka matsa musu lamba a dazuka, inda ya ce:

"Ina so in bayyana a fili cewa wadannan hare-haren ta’addanci yunƙuri ne na ‘yan ta’adda da ke kokarin yada tsoro, kasancewar suna fuskantar matsin lamba mai tsanani daga jaruman sojojinmu da hukumomin tsaro da ke aiki a wurare daban-daban."

Ya kara da cewa:

"Za mu ci gaba da kara zage damtse wajen yaki da dukkan masu aikata laifuffuka, a duk inda suke."

Kara karanta wannan

Abin da ake cewa kan Trump ya gargadi Tinubu bayan harin Maiduguri

Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya

A bayanin da ya yi, shugaban kasa Tinubu ya yaba wa dakarun Najeriya bisa jajircewar da suke wajen yaki da 'yan ta'adda a jihohi daban-daban.

Ya ce:

"Ina yaba wa jarumta da jajircewar sojojinmu masu kishin kasa, wadanda suka samu nasarar dakile hare-haren hadin gwiwa da ‘yan ta’adda suka kai kan sansanonin soja a jihar."
"Hare-haren da aka kai a ranar Litinin ayyuka ne na rashin imani daga kungiyoyin ‘yan ta’adda. Sojojinmu da kuma rundunonin sa-kai za su dakile su kuma su murkushe su gaba daya."
Wajen da aka kai hari Borno
Jami'in tsaro a wajen da aka kai hari Maiduguri. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Batun murkushe Boko Haram

Tinubu ya ce ya umarci hafsoshin tsaro su tafi Maiduguri domin su jagoranci yadda za a shawo kan lamarin tare da umurtar hukumomin agaji su tabbatar an kula da wadanda suka jikkata yadda ya kamata.

Ya ce:

"Babu wani wuri a Najeriya da ‘yan ta’adda za su samu mafaka. Za mu gano su, mu fuskance su, kuma mu murkushe su gaba daya."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tura sako ga Shugaban ƙasa game da harin bama bamai a Maiduguri

Da gaske Trump ya gargadi Tinubu?

A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta sun yada wani sako da ake ikirarin cewa Donald Trump ne ya gargadi Bola Tinubu.

A sakon, an ce Trump ya nemi Bola Tinubu ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Birtaniya saboda hare-haren da aka kai Maiduguri a jihar Borno.

A kokarin tabbatar da gaskiyar abin da ke faruwa, Legit Hausa ta gudanar da bincike na musamman domin tabbatar da sahihancin labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng