Bukukuwan Sallah: Jerin Gwamnonin Arewa 5 da Za Su Biya Albashin Maris da Wuri

Bukukuwan Sallah: Jerin Gwamnonin Arewa 5 da Za Su Biya Albashin Maris da Wuri

A daidai lokacin da watan Ramadan ke shirin ƙarewa, gwamnonin wasu jihohi a Najeriya sun dauki wasu matakai na rage wa ma'aikata raɗadin tattalin arziki da kuma ba su damar yin shirye-shiryen bikin ƙaramar Sallah cikin jin daɗi.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Aƙalla gwamnoni biyar ne suka ba da umarnin biyan albashin watan Maris a tsakiyar wata ga dukkan ma'aikatan gwamnati da masu karɓar fansho, sabanin karshen wata da aka saba biya.

Wasu gwamnonin Arewa 5 sun ba da umarnin biyan albashin watan Maris da wuri don bikin karamar Sallah.
Hagu zuwa dama: Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu; gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, da gwamnan Kano, Abba Yusuf. Hoto: Ahmad Aliyu/Dauda Lawal/Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Wannan mataki ya biyo bayan ƙoƙarin tabbatar da cewa ma'aikata sun samu isassun kuɗaɗe a hannunsu domin gudanar da sayayya da sauran dawainiyar iyalansu kafin ranar Sallah, cewar rahoton Daily Trust.

Bikin ƙaramar Sallah na zuwa ne bayan kammala azumin kwanaki 30 ko 29, wanda lokaci ne na farin ciki da nuna godiya ga Ubangiji.

Kara karanta wannan

Rabon shinkafar Tinubu: Yadda ake 'bambance' Kudu da Arewa wajen tallafa wa mutane

Gwamnonin da za su biya albashi da wuri

1. Zamfara

A jihar Zamfara, kwamishinan yaɗa labarai da al'adu, Muhammad Dantawasa, ya sanar da cewa gwamnati ta amince da fara biyan albashin watan Maris cikin gaggawa.

Wannan na zuwa ne a matsayin tallafi ga ma'aikata domin su fuskanci bukukuwan Sallah ba tare da fargabar rashin kuɗin sayen kayan masarufi ko tufafi ga yaransu ba, in ji rahoton Punch.

2. Sokoto

Ita ma jihar Sokoto, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu, ta ba da sanarwar fara biyan albashin tun a ranar Juma'a, 13 ga Maris, 2026.

Gwamnan ya bayyana cewa biyan albashin a wannan lokaci zai taimaka sosai wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a jihar, yayin da ma'aikata za su garzaya kasuwanni domin yin shirye-shiryen Sallah.

3. Kano

A jihar Kano kuwa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin biyan albashin ga ma'aikata da 'yan fansho tun kafin karshen watan Maris, in ji rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

"Yan ta'adda na amfani da bidiyon azabtarwa don firgita al’umma": Masani ya bayar da mafita

Bilkisu Shehu Maimota, wadda ita ce mukaddashiyar shugabar ma'aikatan gwamnati ta jihar, ta jaddada cewa wannan mataki zai tabbatar da cewa kowane ma'aikaci ya yi Sallah cikin walwala da iyalinsa.

A jihar Kogi, Gwamna Usman Ododo ya ba da umarnin biyan albashin Maris cikin gaggawa.
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo. Hoto: @OfficialOAU
Source: Facebook

4. Kogi

Haka zalika, jihar Kogi ƙarƙashin Gwamna Usman Ododo ta amince tare da sakin kuɗaɗen albashin watan Maris, kamar yadda aka wallafa a shafin gwamnatin jihar.

Wannan na daga cikin matakan jin ƙai na gwamnatin Ododo domin taya ma'aikatan jihar murnar nasarar kammala azumin Ramadan da shiga watan Shawwal.

5. Kebbi

A ƙarshe, Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi shi ma ya ba da umarnin fara biyan dukkan ma'aikatan jihar albashinsu na watan Maris cikin gaggawa.

Gwamnan, wanda tsohon shugaban ƙungiyar ƙwadago ne, ya san muhimmancin samun albashi a kan lokaci musamman a irin wannan lokaci na hidimomin sallah.

Abin da wasu ke fada kan haka

Legit Hausa ta zanta da Usman Abdullahi daga karamar hukumar Maru, jihar Zamfara, wanda ya ce abin da Gwamna Dauda ya yi abin a yaba ne, duk da cewa nauyi ne ya sauke.

"Kasan mutane suna manta cewa, shi biyan albashi nauyi ne na gwamnati, dole ne ta sauke wannan nauyin, gode mata don ta biya albashi ba shi da fa'ida.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe Boko Haram kusan 100 suna shirin kai hari ana gobe sallah

"Amma, abin da Gwamna Dauda ya yi abin a yaba ne. Ya yi albashi a daidai lokacin da mutane ke bukatar kudin don shirin Sallah. Wanda zai sanya a samu saukin ciwo bashi."

- Usman Abdullahi.

Shi ma Nasir Abbas Garkuwa, daga jihar Sokoto, ya shaida wa Legit Hausa cewa:

"Alhamdulillah, dama hakan aka san shugaba da tausayi. A duk lokacin da wata hidimar al'umma irin wannan ta taso, to sai a yi albashi da wuri, don mutane su shiga walwala. Allah ya saka masa da alheri."

Saudiyya ta ayyana ranakun hutun Sallah

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin kasar Saudiyya ta fitar sanarwa game ranakun gudanar da sallar idi a wanann shekara ta 2026.

Ƙasar ta sanar da hutun idin karamar sallah ga ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu domin ba su damar shirya bukukuwa.

Rahoto ya nuna cewa ranar idi za ta dogara ne da ganin jinjirin watan Shawwal; idan Ramadan kwanaki 29 ne, Sallah za ta fara 19 Maris, 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com