Abu Ya Girma: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Filin Jirgin Sama, an Kama 4

Abu Ya Girma: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Filin Jirgin Sama, an Kama 4

  • Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta tabbatar da kama wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a filin jirgin saman Akure
  • FAAN ta bayyana cewa an kama mutane hudu daga cikin wadanda ake zargi yayin da aka hango daya daga cikinsu na shirin sulalewa
  • Ta tabbatar da cewa an kama mutanen ne bayan jami'an tsaro sun yi hadin gwiwa, kuma za ta cigaba da kawar da barazanar 'yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta tabbatar da kama wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan bindiga ne a filin jirgin saman Akure da ke jihar Ondo.

Rahotanni da kafafen yada labarai suka wallafa sun nuna cewa an kama mutanen ne bayan wani samame na hadin gwiwa da jami’an tsaro suka gudanar.

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Abuja Kaduna dauke da fasinjoji ya gamu da hatsari, an samu bayanai

Taswirar jihar Ondo
Taswirar jihar Ondo a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Legit Hausa ta tattaro bayanan da hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya ta yi ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.

'Yan bindiga sun shiga filin jirgin sama

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar kula da jiragen sama ta kasa (FAAN), Henry Agbebire, ya sanar da cewa wasu 'yan bindiga sun shiga filin jirgin saman Akure da ke jihar Ondo.

Hukumar FAAN ta bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne bayan jami’an tsaro sun samu rahoton gaggawa kan wani motsi da ake zargi na su ne a kusa da shingen filin jirgin, kusa da unguwar Eleyewo.

Sanarwar ta ce nan take jami’an tsaro suka kaddamar da wani samame na hadin gwiwa a yankin, wanda ya hada da jami’an tsaron jiragen sama na FAAN (AVSEC) da sojojin saman Najeriya.

Wasu 'yan bindiga yayin sulhu a Katsina
Ado Aliero da wasu 'yan bindiga a jihar Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Rahoton da tashar TVC ta wallafa ya nuna cewa sojojin kasa, ‘yan sandan Najeriya da kuma kungiyoyin tsaron sa-kai na yankin sun shiga cikin samamen.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Ana cikin musayar wuta, an kama masu yiwa Iran zagon kasa a yaki da Amurka

'Yan bindigan sun nemi guduwa

Agbebire ya bayyana cewa wasu daga cikin wadanda ake zargin sun yi yunkurin tserewa bayan sun ga jami’an tsaro, amma an yi nasarar kama mutane hudu daga cikinsu.

Jami'in FAAN ya kara da cewa an mika wadanda aka kama ga rundunar 'yan sandan Najeriya domin ci gaba da yi musu tambayoyi da bincike

FAAN ta yabawa jami'an tsaro

FAAN ta yaba da hadin gwiwar gaggawa da jami’an tsaron jiragen sama, sojoji, ‘yan sanda, kungiyar tsaro ta Amotekun da kuma masu gadi suka nuna, tana mai cewa hakan ya kai ga samun nasarar kama wadanda ake zargi.

Hukumar ta kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kara kaimi wajen inganta tsaro a filayen jiragen sama a fadin kasar nan domin kare matafiya.

An farmaki Malamin Izala a Gombe

A wani labarin, kun ji cewa an samu tarnaki da ya hada da sakataren majalisar malaman kungiyar Izala a karamar hukumar Nafada a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi fariya, ta fadi nasarar da ta samu a kan fadar Ayatollah Khamenei

Wasu matasa da ake zargin 'yan Darika ne sun kai farmaki masaukin Malam Abubakar Puma da Izala ta tura tafsiri karamar hukumar.

Matasa da 'yan agaji sun kai dauki domin tabbatar da ba a kashe malamin ba, inda daga baya 'yan sanda suka ce ko mutum daya bai rasu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng